Camavinga zai yi jinya har bayan karshen kakar nan

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Real Madrid, Eduardo Camavinga zai yi jinya har zuwa karshen kakar bana.
Ɗan kwallon tawagar Faransa ya ji rauni ranar Laraba a wasan da Real Madrid ta ci Getafe 1-0 a wasan La Liga.
An sauya Camavinga daga karawar a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, yayin da Real Madrid ta sanar cewar zai yi jinyar watanni.
Kenan Camavinga, wanda ya yi wa Real Madrid wasa 34 a dukkan karawa a bana, ba zai buga mata Copa del Rey ba da za ta fafata da Barcelona.
Ranar Asabar za a buga wasan hamayya a wasan karshe a Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid a Sevilla.
Haka kuma Camavinga ba zai samu buga wa Real Madrid gasar kofin zakarun nahiyoyin duniya ba da ake kira Club World Cup da za a yi daga Yuni zuwa Yuli ba.
Wannan raunin da Camavinga ya ji, zai zama koma baya ga Real Madrid, bayan da ake tantama kan koshin lafiyar Kylian Mbappe da Ferland Mendy da kuma David Alaba.
Real Madrid tana mataki na biyu a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Barcelona mai jan ragama, kuma saura wasa biyar-biyar a kammala babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta kakar nan.
Tuni aka yi waje da Real Madrid a Champions League, bayan da Arsenal ta doke ta 5-1 gida da waje a zagayen kwata fainal.











