Babban sakataren OPEC Sanusi Barkindo ya rasu

Muhammadu Barkindo, OPEC Sec. Gen
An wallafa

Allah Ya yi wa Babban Sakataren Kungiyar kasashen da ke arzikin man fetur, OPEC, Dr Muhammad Sanusi Barkindo rasuwa a ranar Talata da daddare.

Rasuwarsa ta zo farat ɗaya, inda ko a ranar Talatar da rana ya kai wa Shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja, tare da tawagar shugabannin Kungiyar OPEC.

 

Margayi Sanusi Barkindo na shirin sauka saga mukaminsa na sakataren OPEC bayan shafe shekaru shida a kan kujerar.

Shugaban Kamfanin mai na Najeriya, NNPC, Malam Mele Kyari ne ya sanar da rasuwar marigayi Barkindo a wani sakon da ya wallafa ranar Laraba da asuba a shafinsa na Twitter.

 

Ana sa ran yin za a fitar da bayanai game da shirin jana’izar margayin a ranar.

 

Wane ne Sanusi Barkindo?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An haifi Mohammed Sanusi Barkindo a watan Afrilun shekarar 1959.

Ya riƙe mukamai daban-daban kamar muƙaddashin Sakatare Janar na ƙungiyar ƙasashe masu arzikin man fetur ta OPEC a 2006.

Ya zama wakilin Najeriya a kwamitin kula da harkokin tattalin arziki na hukumar OPEC daga shekarar 1993 zuwa 2008.

A shekarar 2009 ya zama shugaba kamfanin man fetur na Najriya NNPC har zuwa 2010.

Ya taɓa jagorantar tawagar ƙwararru ta Najeriya zuwa taron Majalisar Dinkin Duniya na yarjejeniya kan sauyin yanayi a 1991.

Barkindo ya kammala digirinsa a kan kimiyyar siyasa a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria a 1981.

Ya yi babbar difloma a kan tatalin arzikin albarkatun man fetur a Jami'ar Oxford ta Birtaniya a 1988.

Sannan ya yi digiri na biyu a Jami'ar Washington a 1991 kan sha'anin kasuwanci.

Kuma Jami'ar Fasaha ta Tarayya ta Yola ta ba shi digirin girmamawa.

Barkindo ya taba rike mukamin mataimakin manajan darakta na kamfanin Nigerian Liquefied Natural Gas, LNG.

Mohammed Sanusi Barkindo ya rike mukamai daban-daban a ƙungiyar Opec daga 1986 zuwa 2010.

Shugabannin NNPC da suka rasu a baya-bayan nan

Barkindo shi ne na uku cikin tsofaffin shugabannin kamfanin man fetur na Najeriya da suka rasu a baya-baya nan.

Mai Kantu Baru

A ranar 30 ga watan Mayun 2020 ne Allah Ya karbi rayuwar Mai Kantu Baru.

Ya rasu yana da shekara 60 a duniya bayan ƴar gajeriyar rashin lafiya.

Shi ne shugaban NNPC na 18, inda ya riƙe shi daga 2016 zuwa 2019.

Dr Dahwa

A ranar 3 ga watan Agutstan 2020 ne kamfanin mai na NNPC ya sanar da rauwar tsohon shugabansa Joseph Dawha.

Dr Dahwa shi ne shugaban NNPC na 16. Kuma ya jagoranci kamfanin daga Agustan shekarar 2014 zuwa Agustan 2015.

Sanusi Barkindo

Ya rasu a ranar Talata 5 ga watan Yulin 2022.

Ya jagoranci kamfanin NNPC daga shekarar 2009 zuwa 2010.