An dage wasanni a Birtaniya saboda mutuwar Sarauniya

Asalin hoton, Reuters
An dage duka wasannin kwallon kasafar yankunan Wales da Nothern Irelanda da Scottland saboda mutuwar Sarauniya Elizabeth II.
An soke wasannin 10 na Premier Ingila da shida na Scottland da aka tsara yi a wannan makon a baya.
Wasan gasae Ingila da aka tsara yi a ranar Asabar da Juma'a, da wasan mata guda shida da farkon wannan kakar duka an soke su.
Wasannin kasar Ingila da na FA na kuma na kananan kungiyoyin kwallon kafa an soke su.
Za a koma wasan kureket a ranar Asabar mai zuwa wanda zai gudana tsakanin Ingila da Afrika Ta Kudu, sai wasan mata na IT20 shima za a yi a ranar tsakanin Indiya da Ingila.
A a buga wasannin Golf PGA a ranar Asabar bayan dakatar da shi da aka yi a ranar Alhamis.
Za a koma wasannin tseren doki na Birtaniya a sanar Lahadi yayin da za a fara na zari ruga a ranar Asabar bayan dage wasanni biyu da aka yi a ranar Juma.
Na dage fafatawar duniya ta wasan damben Boxing tsakanin Savannah Marshall da Claressa Shields, yayin da aka sanya ranar 15 ga watan oktoba domin sake tsayar da ranar wasan.
An dage duka wasannin Boxing da aka tsara yi a karshen mako.
Sarauniya Elizabeth II ita ce mafi dadewa a kan karagar mulkin Birtaniya ta kuma mutu ne a ranar Alhamis tana da shekara 96 a duniya, bayan kwashe shekara 70 tana jagoranci.











