N'Golo Kante ba zai buga gasar kofin duniya ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Chelsea, N'Golo Kante ba zai wakilci Faransa ba a gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar, bayan da aka yi masa aiki kan raunin da ya ji.
Kante mai shekara 31, ya ji rauni a wasan da Chelsea ta tashi 2-2 da Tottenham ranar 14 ga watan Agusta a Stamford Bridge.
Kociyan Chelsea, Graham Potter ya fada a baya cewar kafin su kara da Aston Villa a makon jiya, dan kwallon ya ci karo da koma baya.
Kante ya lashe kofin duniya tare da Faransa a 2018 a Rasha, ya shiga jerin 'yan wasan Premier da suka ji rauni mai muni a lokacin da ake shirin gasar kofin duniya.
Za a fara wasannin babbar gasar tamaula ta duniya a Qatar daga 20 ga watan Nuwamba, inda tawaga 32 za su fafata a tsakaninsu a karon farko a tarihi.
Shima dan wasan Chelsea, Reece James na fuskantar kalubale, wanda ya ji rauni a Champions League da kungiyar Stamford Bridge ta ci Milan a watan jiya.
Ranar Talata Liverpool ta sanar da cewar Diogo Jota zai yi jinya mai tsawo, kenan ba zai buga wa Portugal gasar kofin duniya ba.





