Inter Miami za ta ɗauko Kevin de Bruyne, Manchester United na zawarcin Matheus Cunha

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na neman sayen ɗan wasan gaban Wolves da kuma Brazil mai shekara 25, Matheus Cunha (Talksport)
Tottenham Hotspur za ta ɗauki ɗan wasan gaban RB Leipzig da Jamus mai shekara 29, Timo Werner, idan wa'adin zaman sa a matsayin ɗan wasan aro ya ƙare a bana. (Fabrizio Romano)
Chelsea ta janye daga zawarcin ɗan wasan gaban Napoli da Najeriya mai shekara 26, Victor Osimhen, kuma hakan na nufin a yanzu Manchester United ce kaɗai ke bibiyar ɗan wasan. (CaughtOffside)
Inter Miami na shirin ɗauke ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Belgium mai shekara 33, Kevin de Bruyne, amma tana fuskantar ƙalubale daga ƙungiyoyin Saudiyya. (Mirror)
Matashin ɗan wasan Ingila mai shekara 20, Jamie Gittens, 20, na son barin Borussia Dortmund a ƙarshen kakar wasan bana, kuma ƙungiyoyin gasar Firimiya da dama na bibiyar shi. (Sky Germany - in German)
Everton da Brighton sun shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan gaban Ingila da Ipswich mai shekara 22, Liam Delap, wanda zai bar Ipswich idan ta kasa ci gaba da taka leda a gasar firimiya . (TeamTalk)
Fiorentina za ta tsawaita kwangilar mai tsaron ragar Sifaniya mai shekara 34, David de Gea, lamarin da zai bata damar riƙe ɗan wasan har nan da watan Yunin 2926. (Fabrizio Romano)
Leicester City na shirin korar kocinta, Ruud van Nistelrooy bayan an doke ƙungiyar har sau 9 a jere. (Football Insider)
Bayer Leverkusen na bibiyar mai tsaron ragar Brentford da Netherlands mai shekara 31, Mark Flekken, (Sky Germany - in German)















