Za a bayar da tikiti 18,000 ga wadda ta kai wasan karshe a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Duk ƙungiyar da ta kai wasan karshe a Champions League a bana, za a ba ta tikiti 18,000 da zai kama kan farashin £60.

Za a buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai ta bana a watan Mayu a Munich, kuma babban farashin tikitin da za a bai wa ƙungiya ya kai daga £800.

Kuma ƙungiya ɗaya ce daga biyu da suka rage daga Premier League za ta yi zuwa wasan karshe da za a buga ranar 31 ga watan Mayu, idan ta sa ƙwazo.

Ranar Litinin UEFA ta sanar cewar tikiti 38,700 ta tanada ga ƙungiya a wasan karshe daga 64,500 da ta samar, wato kaso 60 cikin 100.

Kenan tikiti 36,000 za a sayar ga ƴan kallo har da wanda za a sayar ga masu bukata ta musamman.

Farashin tikitin ya kama daga £60 da £154 da kuma £813, ya dangan ci wajen da mutum zai zauna.

Arsenal da Aston Villa ne suka raga a Champions League a bana daga Premier League, inda Arsenal za ta kara da Real da na PSG da Aston Villa.

Haka kuma Tottenham da Manchester United da Rangers suna buga Europa League daga Birtaniya.

Saboda haka wasan karshe da za a yi a Bilbao ranar 21 ga watan Mayu, an tanadi tikiti 41,000 a wasan karshe daga 49,000, sama da kaso 80 cikin 100 kenan.

Chelsea wadda take buga Conference League daga Premier League, za ta yi fatan kai wa zagayen karshe ranar 28 ga watan Mayu a Wroclaw a Poland.

Kenan an tanadi tikiti 12,500 daga 35,000 a wasan karshe kan farashi daga £21.