Hikayata 2023: Labarai 15 da suka ciri tuta

Alkalan gasar rubutun kagaggun labarai ta mata zalla ta BBC Hausa wato Hikayata sun kammala tantance labarai 15 da suka ciri tuta.
Hakan na nufin alkalan sun fita da guda uku da su ne zakaru sai kuma guda 12 da suka cancanci yabo.
Mata kusan 500 ne dai suka shiga wannan gasa, inda a matakin farko aka tantance labaran zuwa 400, kafin daga bisani a mataki na biyu na tantancewa wasu alkalai da ba ma'aikatan BBC ba ne suka zabi guda 30.
Wata tawagar alƙalan a mataki na karshe, bisa jagorancin ma'aikacin BBC sun zaɓi labaran 15 daga cikin 30 sannan kuma sun zabi gwarazan da labarinsu ya yi nasarar yin na ɗaya da na biyu da na uku.
Har wa yau, sun kuma ware guda 12 da suka ce sun cancanci yabo.
Ga jerin labaran 15 da suka ciri tuta tare da sunayen marubuta. To sai dai ba a wallafa su ba tsarin lamba:
- Duniyar Mafarkina - Sumayyah Abdulkadir Takori
- Mairamu – Fatima Kabir
- Batan Dabo – Hadiza Ibrahim D. Auta
- Tsalle Daya – Hadiza Ibrahim Mshelia
- Rina A Kaba - Aisha Adam Hussaini
- Bakin Kishi - Aisha Abdullahi Yabo
- Hakorin Dariya - Rabi’atu Ahmad Mua’zu
- Tuwon Kasa – Aisha Sani Abdullahi
- Rabon Kwado - Fa'iza Abubakar
- Kazar Wahala – Fatchima Oumarou Abdou
- Cizon Yatsa - Aisha Adam
- Matar Aljanna - Nafisa Rabiu Umar
- Abincin Wani - Aisha Nalado
- Labarin Maryam - Jamila Lawal
- Karshen Wahala - Zainab Muhammad Chubaɗo
Waɗanda su ka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan daya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu dari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu dari biyar) ga wadda ta zo ta uku.
BBC za kuma ta watsa labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.
Za a sanar da mutum ukun da suka zamo zakaru a yayin wani bikin karramawa a Abuja, babban birnin Najeriya, ranar 30 ga watan Nuwamban nan na 2023.
Hikayata gasa ce ta ƙagaggun gajerun labarai wadda ke samar da dama ga mata marubuta, waɗanda ba su ƙware ba da kuma ƙwararru don nuna fasaharsu da ba da damar karanta labaransu a harshen Hausa.












