Amurka da Isra'ila sun yi watsi da tsarin ƙasashen Larabawa na sake gina Gaza

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, David Gritten
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
Amurka da Isra'ila sun yi watsi da tsarin ƙasashen Larabawa na sake gina Zirin Gaza, wanda zai sa Falasɗinawa su koma su ci gaba da zama a zirin domin ci gaba da rayuwarsu.
Tsare-tsaren, waɗanda shugabannin ƙasashen Larabawa suka cimma a Cairo, sun zama madadin wanda Shugaban Ƙasa Donald Trump ya kawo na ƙwace iko da Gaza, da kuma sauya musu matsuguni.
Hukumomin Falasɗinu da Hamas sun yi maraba da matakin na ƙasashen Larabawa, wanda ya buƙaci yankin Gaza ya kasance ƙarƙashin kulawar wani kwamiti na wucin-gadi da za a zaƙulo mambobinsa daga ƙwararrun masu shiga tsakanin na ƙasashen duniya.
Amma Amurka da ministan harkokin wajen Isra'ila sun ce tsarin bai fayyace hanyoyin magance matsalolin da Gaza ke fuskanta ba, wanda hakan ya sa suka fi amincewa da tsarin Trump.
Shugabannin ƙasashen Larabawan sun yi taron ne bayan an ga yadda yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ke tafiya hawainiya, har ake fargabar za ta iya lalacewa bayan zango na farko wanda aka yi mako shida ana yi ya kawo ƙarshe.
Isra'ila ta hana shigar da kayan agaji Gaza domin tilasta wa Hamas amincewa da sabon tsarin na Amurka na tsawaita yarjejeniyar domin samun ƙarin lokacin da za a yi musayar waɗanda Hamas ke riƙe da su a Gaza da fursunonin Falasɗinawa.
Ita kuma Hamas ta dage kai da fata sai dai a shiga zango na biyu na yarjejeniyar kamar yadda aka tsara, wanda zai kawo ƙarshen yaƙin, da kuma janye sojojin Isra'ila daga yankin.
A ranar Talata ce ƙasar Masar ta gabatar da tsarin sake gina Gaza da zai ci dala biliyan 53 wato kimamin fam biliyan 41 a wani taron gaggawa na ƙasashen Larabawa.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A wata sanarwa da suka fitar bayan taron, sun nanata watsi da, "duk wani yunƙurin sauya wa Falasɗinawa," inda suka ce hakan, "yi wa dokokin ƙasa da ƙasa karan-tsaye ne da cin zarafin ƴanadam da yunƙurin kisan ƙare dangi."
Larabawan sun tsare sake gina zirin ne mataki uku wanda za a yi a cikin shekara biyar, inda mutanen yankin guda miliyan 1.5 za su koma zirin su koma shiga gidaje 200,000 da aka gina, da guda 60,000 da aka gyara.
A zagaye na farko wanda zai yi wata shida, za a kashe dala biliyan 3 ne wajen share baraguzan da suka mamaye zirin.
Zagaye na biyu kuma wanda za a ɗauki shekara biyu ana yi, zai ci kuɗi dala biliyan 20, kuma za a sake gina gidaje da fili jirgin sama da filin jirgin ruwan sama, sannan a gina yankin masana'antu a zagaye na uku wanda zai ci dala biliyan 30 a cikin shekara biyu.
Hamas - wadda Isra'ila da Amurka da Birtaniya suka ayyana a matsayin ƴan ta'adda- sun ƙwace iko da Gaza ne a shekarar 2007 daga hannun PT na Fatah. Sai PA ɗin suka cigaba da mulkin wasu ɓangarorin na gaɓar yamma da tekun Jordan.
Shugaban yankin Falasɗinu, Mahmoud Abbad, wanda yake jagorantar PA, ya bayyana wa shugabannin ƙasashen Larabawa cewa suna maraba da matakin, sannan ya yi kira ga Trump da ya ba su goyon baya.
Hamas ta ce tana maraba da "matakin shugabannin ƙasashen Larabawa na dakatar da yunƙurin korar mutanensu."
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba ya cikin duk wani tsari da za a yi a Gaza domin Hamas ko PA.

Asalin hoton, EPA
Sai dai firaministan Isra'ila ya yi watsi da matakin, inda ya ce, "ba su magance asalin matsalolin da suka biyo bayan harin 7 ga Oktoban 2023 ba.
"Tsarin Trump ya fi kyau, domin zai ba mutanen yankin Gaza su samu abubuwan da suke so. Ya kamata mu ƙarfafa masa gwiwa," in ji shi.
"Maimakon a gwada, sai ƙasashen Larabawa suka yi watsi da tsarin, kuma suka cigaba da zargin Isra'ila ba tare da hujja ba."
Shi ma kakakin ofishin tsaro na Amurka, Brian Hushes ya ce tsarin Larabawa bai warware "matsalolin da Gaza ke fuskanta ba, kasancewar yanzu Gaza baraguzai ne kawai kuma bai kamata mutane su rayuwa a yankin da ke cike da baraguzai ba da ma bama-baman da suke ƙarƙashin ƙasa."
"Shugaba Trump a shirye yake ya sake gina Gaza, tare da fatattakar ƴan Hamas. A shirye muke mu cigaba da tattaunawa domin ganin dawo da zirin yadda yake."
Trump ya bayar da shawara a watan jiya cewa Amurka "za ta karɓe iko" da Gaza sannan za ta sauya wa mutanen matsuguni, ta yadda za a sake gina zirin domin ya koma abin da ya kira "Riviera of the Middle East".
Ya ce waɗanda suka riga suka tsere ba sai sun dawo ba saboda yanzu sun samu "matsugunin da suka fi kyau" a Masar da Jodan da wasu ƙasashen.

Asalin hoton, AFP
Mataimakin sakatare janar na ƙungiyar ƙasashen Larabawa, Hossa Zaki ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa ba za su amince da tsarin Trump ba.
Mutanen yankin Falasɗinu na fargabar sake aukuwar Nakba -kalmar larabci da ke nufin bala'i - da aka shiga a baya lokacin da dubban mutanen yankin suka bar muhallansu a lokacin yaƙin da ya ɓarke bayan an ƙirƙiri ƙasar Isra'ila a shekarar 1948.
A ƙarshe dai sai wasunsu suka ƙare a Gaza. Sanna kuma aƙalla masu gudun hijira 900,000 suka cigaba da zama a yankin gaɓar yamma da tekun Jordan, sannan mutum miliyan 3.4 suka koma rayuwa a Jordan da Syria da Lebanon, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta nuna.
Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi ne domin kawo ƙarshen Hamas a matsayin martani ga harin ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda aka kashe kusan Isra'ilawa 1,200, sannan aka yi garkuwa da 251.
Sama da mutum 48,000 ne aka kashe a Gaza tun daga lokacin kamar yadda ma'aikatar lafiyar Hamas ta ruwaito.











