Arsenal na farautar Coman, Ko Ederson zai bar Man City?

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na shirin karɓo aron ɗanwasan gaba na na Faransa Kingsley Coman yayin da kuma a shirye Bayern Munich take ta saki ɗanwasan mai shekara 28. (Football Insider)
Kungiyoyin Saudiyya na sa ido kan ɗanwasan gaba na Brentford Ivan Toney, kuma Al-Ahli na gaba da ke neman ɗanwasan na Ingila mai shekara 28. (Fabrizio Romano)
Newcastle United na son ƴarwasan gaba ta Manchester United Nikita Parris, mai shekara 30, yayin da ƙungiyar ke son haurowa gasar mata ta Super League. (Guardian)
Stuttgart na son sayen ɗanwasan da ta karɓo aronsa daga Chelsea, Armando Broja inda ɗanwasan na Albania mai shekara ya nuna sha’awar ci gaba da taka wa ƙungiyar ta Jamus leda. (Sky Sports Germany)
AC Milan na son karɓo aron ɗanwasan Roma mai shekara 26 Tammy Abraham amma tana fuskantar hamayya daga Bournemouth, Everton da kuma Leicester City. (Calciomercato - in Italian)
Nottingham Forest ta yi watsi da tayin Atalanta na fam miliyan 17 kan ɗanwasanta na Wales Neco Williams, mai shekara 23. (Fabrizio Romano)
Ɗanwasan baya na Liverpool Virgil van Dijk shekara ɗaya ta rage masa a ƙungiyar kuma ɗanwasan na Netherlands mai shekara 33 ya ce babu alamun tsawaita yarjejeniyar. (Liverpool Echo)
Golan Brazil Ederson, mai shekara 30, ana alaƙanta shi da ƙungiyoyin Saudiyya amma ya ce zai ci gaba da wasa a Manchester City bayan tattaunawa da Pep Guardiola. (Mirror)
Leicester City ta taya ɗanwasan gaba na Panathinaikos da Greece Fotis Ioannidis kan sama fa fam miliyan 17 a yayin da ƙungiyar ke tattaunawa domin karɓo ɗanwasan gaba na Ivory Coast Wilfried Zaha, mai shekara 31, daga Galatasaray. (Telegraph - subscription required)
Brentford ta amince da yarjejeniyar karɓo ɗanwasan tsakiya na Sweden Jens Cajuste daga Napoli tare da fatan sayen ɗanwasan bisa ƙwazonsa. (Football Insider),
Borussia Dortmund na dab da kammala cinikin matashin ɗanwasan gaba na Jamus mai shekara 21 Maximilian Beier daga Hoffenheim kan yarjejeniyar kuɗi sama da fam miliyan 25 . (Sky Sports Germany)










