Sanchez ya sake komawa Udinese

Alexis Sanchez

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Tsohon ɗan wasan Arsenal da Manchester United, Alexis Sanchez ya sake komawa Udinese - bayan shekara 18 rabonsa da ƙungiyar.

Ƙwantiragin ɗan wasan mai shekara 35 ce ta kare a Inter Milan a karshen watan Yulin 2024.

Sanchez, wanda ya taka leda a Udinese tsakanin 2006 zuwa 2011, ya saka hannu kan ƙunshin yarjejeniyar kaka biyu.

Ya ci ƙwallo 80 a wasa 166 a Arsenal bayan da ya koma Emirates daga Barcelona a 2014, amma guda huɗu ya zura a raga a karawa 45 a United a 2018.

Daga nan ne Sanchez ya je buga wasannin aro a Inter a 2019 daga baya ƙungiyar ta mallaki ɗan ƙwallon.

Bayan ya raba gari da Inter a 2022, sai ya koma Marseille daga baya ya koma Inter, wanda ya bayar da gudunmuwar da ta lashe Serie A a bara.

Udinese ta kare a matakin ta shidan karshen teburin Serie A a kakar da ta wuce.