Liverpool ta amince ta sayar da Carvalho ga Brentford

Fabio Carvalho

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Liverpool ta amince ta sayar da Fabio Carvalho ga Brentford kan £27.5m har da karin tsarabe-tsarabe.

Ƙungiyar Anfield ta ɗauki ɗan wasan daga Fulham kan £5m a 2022, kuma Fulham za ta samu kaso 20 cikin 100 a cinikin sayar da shi ga Brentford.

Tun farko Southampton ce ta yi kokarin sayen ɗan wasan, amma tayin da ta yi bai kai wanda Brentford za ta biya ba.

Mai shekara 21 ya taka rawar gani a wasannin sada zumunta da Liverpool ta buga a Amurka a watan nan, wanda ya ci Arsenal da Manchester United.

To sai dai da ƙyar ne idan matashin zai samu damar buga wasannin da yawa a bana, bayan da manyan ƴan ƙwallo suka koma Liverpool, bayan hutu daga Euro 2024 da Copa America.

Carvalho ya buga wasannin aro a bara a RB Leipzig da Hull City, wanda ya ci ƙwallo tara a fafatawa 20 a Hull City.