Waiwaye: Ƙara kuɗin aikin Hajji da miƙa ɗaliban Kuriga ga iyayensu

An wallafa

Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi.

Dalilin Najeriya na ƙara kusan naira miliyan biyu ga maniyyatan Hajji

Aikin Hajji

Asalin hoton, NAHCON

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya.

Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata.

Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya naira miliyan takwas, saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu.

Hukumar ta kuma ba maniyyata aikin Hajjin na bana wa'adin zuwa 29 ga watan nan na Maris da ake ciki domin kammala biyan kudin: " Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa."

Gwamnatin Kaduna ta miƙa ɗaliban Kuriga hannun iyayensu

Kaduna

Asalin hoton, KSG

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce da miƙa ɗaliban makarantar Kuriga da aka sace ga iyayensu.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun gwamnan jihar Sanata Uba Sani ya ce sai da aka tabbatar da lafiyar kwakwalwar yaran da kuma lafiyar jikinsu gabanin a miƙa su ga iyayensu sannan su koma makaranta.

Gwamna Uba Sani ya ce yaran da suka saba da shi suke ɗaukarsa tamkar mahaifi a gare su, sun yi alƙawarin amfani da wannan jarrabawa da suka fuskanta wajen mayar da hanakali da jajurcewa kan karatunsu da sun koma makaranta.

"Gidauniyar Uba Sani za ta ci gaba da kula da karatunsu daga nan har matakin gaba da sakandire," in ji sanarwar.

Tinubu ya bai wa iyalan sojojin da aka kashe gidaje da tallafin karatu

Tinubu

Asalin hoton, Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi alƙawarin kyautar gidaje da kuma tallafin karatu ga iyalan sojojin da aka kashe a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.

Tinubu ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a yayin jana'izar sojojin, inda ya ce gwamnatinsa ba za ta kyale iyalan waɗannan mutane su walaƙanta ba.

"Mutane ne da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen kare ƙasarsu, domin haka ba za mu bari su walaƙanta ba.

"Gwamnati ta bai wa iyalansu gidajen zama da kuma tallafin karatu ga ya'yansu da suk mutu suka bari.

"Za mu tabbatar sun amfana da duk wani tallafi da iyalan waɗanda suka rasa rayuwarsu suke samu a hukumance," in ji Tinubu.

Tinubu ya umarci ma'aikatar fanso ta ƙasar da ta kammala biyan hakkin iyalan mamatan nan da kwana 90.

An bai wa iyalan mamatan lambar girma da kuma shaida a yayin taron jana'izar tasu.

Babban Bankin Najeriya ya ƙara kuɗin ruwa sau biyu a wata ɗaya

CBN

Asalin hoton, @cenbank/X

Babban Bankin Najeriya ya yi ƙarin kuɗin ruwa da kashi 2 karo na biyu kenan cikin wata ɗaya, inda yanzu ya kai kashi 24.75, a cewar gwamnan bankin Olayemi Cardoso.

Shi ne karo na biyu da CBN ya yi ƙarin a cikin wataƊdaya, bayan ƙara kashi 4 a watan Febrairu.

Shawarar babban bankin wanda shi ne ƙari mafi yawa a cikin kusan shekara biyu, na da nufin taƙaita samun kuɗaɗen jari da rage hauhawar farashi.

Hauhawar farashi a Najeriya yanzu ta kai kashi 31.7, sanadin tsadar farashin abinci da na makamashi, tashin kuɗin sufuri da kuma taɓarɓarewar tsaro a yankunan da ake samar da abinci.

Kayan abincin sun haɗar da burodi da shinkafa da nama da nono da kayan marmari duka sun ninka farashinsu.

Najeriya mafi girman tattalin arziƙi a Afirka na fuskantar tsattsauran yanayin tattalin arziƙi, lamarin da ya ingiza mutane da dama cikin talauci.

An yi sammacin Sheikh Gumi saboda kalamansa kan ƴan bindiga

Sheikh Gumi

Asalin hoton, Facebook

Hukumomin tsaro sun gayyaci fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi saboda kalamansa da kuma kiran da ya yi na a yi wa ƴan bindiga afuwa, kamar yadda rahotanni daga kafofin yaɗa labaran ƙasar suka nuna.

Sheikh Ahmad Gumi, wani tsohon jami'in soja ne da ke Kaduna a arewacin Najeriya kuma ya sha tayin shiga tsakanin hukumomi da kuma ƴan bindiga masu garkuwa da satar mutane don neman kuɗin fansa a ƙasar.

A baya-bayan nan ne aka ba da rahoton cewa malamin ya yi tayin tattaunawa da ƴan bindigar a kan sakin gomman ɗaliban da aka sace a farkon watan nan daga wata makaranta da ke Kuriga a jihar Kaduna.

Sai dai gwamnan Kaduna Uba Sani ya ce babu hannun Sheikh Gumi a sakin ɗaliban.

'Yan sandan Kano sun kama ƴan daba 22 da suka addabi Ɗorayi

Kano

Asalin hoton, Kiyawa/Fb

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 22 da ake zargi riƙaƙƙun ƴan daba ne a unguwar Ɗorayi da ke jihar.

Matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar ranar Laraba.Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda aka ji wa wasu matasa raunuka a arangamar da aka yi.

Cikin wani bidiyo da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ƴan sanda sun bayyana sunan wasu mutum 30 da ake zargi ƴan daba ne da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.

A cewar kakakin rundunar, kwamishinan ƴan sanda na jihar Muhammad Usaini Gumel zai buɗe sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.

Rundunar ta ƙaddamar da shirin tuba da gyara halin wasu 'yan daba a Kano, har ma ta ɗauki wasu kusan 50 aiki bayan sun tuba.

Kazalika, rundunar ta sha shirya wasanni tsakanin tubabbun 'yan dabar da kuma ma'aikatanta a matsayin wani sabon salon yaƙi da halayayyar ta daba.

Kiyawa ya wallafa a shafinsa cewa "wani bidiyo da yake ta yawo a kafafen sada zumunta kan wannan lamari, ba su san shi ba, kuma bidiyon ba a Kano ya faru ba."

Kotu ta sanya wa Murja Kunya takunkumin amfani da soshiyal midiya

Murja

Asalin hoton, Murja Ibrahim Kunya/Fb

Wata babbar kotu da ke Kano ta ba da belin fitacciyar jarumar Tiktok, Murja Ibrahim Kunya a kan kuɗi naira dubu 500 da kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya mata.

Baba Jibo Ibrahim, mai magana da yawun kotunan Kano ya tabbatar wa BBC wannan labarin, inda ya ce kotun ta ba da belin Murja ne bayan zaman kotun da aka yi ranar Litinin.

Alƙalin ya ce dole ne ɗaya daga cikin masu tsaya mata ya zama ɗan'uwanta na jini, sannan ɗayan kuma dole ne ya zama yana da shaidar mallakar fili a Kano.

Alƙali Nasiru Saminu ya kuma ce ya bayar da belinta ne bisa hujjar cewa matashiyar 'yar Tiktok ɗin ta wuce kwana 30 a garƙame.