Real Madrid ta matsu kan Alexander-Arnold, Man Utd na harin Tuchel

Trent Alexander-Arnold

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid ta zaku ta sayi ɗan bayan Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 25, wanda ya rage shekara ɗaya kwantiraginsa ya ƙare a Liverpool. (Talksport)

Ba lalle ba ne Manchester United ta ɗauki tsohon kociyan Ingila Gareth Southgate idan ta rabu da Erik ten Hag. Maimakon haka ana sa ran ƙungiyar ta fi bayar da fifiko ga tsohon kociyan Chelsea Thomas Tuchel. (Mail)

Ita kuwa Newcastle United ta ce za ta yi bakin ƙoƙarinta domin ganin ta riƙe kociyanta Eddie Howe bayan da ake raɗe-raɗin cewa ƙila kociyan mai shekara 46, zai maye gurbin Gareth Southgate a tawagar Ingila. (Guardian)

Aston Villa na son fam miliyan 60 daga Al-Ittihad, idan har ƙungiyar ta Saudiyya na son raba ta da ɗan gabanta Moussa Diaby na Faransa. (Talksport)

Manchester United na tattaunawa da wakilan matashin ɗan bayan Lille, Leny Yoro, mai shekara 18, wanda shekara ɗaya ta rage masa a kwantiraginsa, wanda kuma Real Madrid ke hari, kan buƙatun ɗan wasan na Faransa bayan da suka daidaita a farashin fam miliyan 52. (Guardian)

Marseille ta cimma yarjejeniya ta baka da ta kai fam miliyan 26.7, ta sayen ɗan gaban Manchester United, Mason Greenwood, ɗan Ingila mai shekara 22. (The Athletic )

Aston Villa na shirin gogayya da Chelsea da Barcelona a kan sayen ɗan wasan gaba na gefe na Athletic Bilbao Nico Williams, mai shekara 22, wanda ya yi wa Sifaniya wasa a gasar cin kofin ƙasashen Turai da aka kammala, Euro 2024. (Teamtalk)

Al-Nassr ta kawo ƙarshen cinikin mai tsaron ragar Manchester City Ederson, mai shekara 30, bayan da Cityn ta ƙi tayinta na yuro miliyan 30, abin da ya sa ƙungiyar ta Saudiyya yanzu ta karkata ga cinikin takwaransa na Brazil Bento, wanda ke wasa a Athletico Paranaense. (Fabrizio Romano)

Arsenal na sa ran samun ƙarin tayi a kan ɗan wasanta na tsakiya Emile Smith Rowe bayan da ta ki yarda da tayin Fulham , inda yanzu Crystal Palace ma ke son ɗan wasan ɗan Ingila. (Evening Standard)

Cole Palmer ya yi ƙoƙarin shawo kan abokin wasansa na Ingila, kuma ɗan gaban Aston Villa Ollie Watkins, mai shekara 28, a kan ya koma Chelsea a bazaran nan. (Football Insider)

Leicester City ta gabatar da tayin fam miliyan 21 da ƙarin wasu tsarabe-tsarabe na fam miliyan 4 a kan ɗan wasan tsakiya na Argentina Matias Soule, mai shekara 21, to amma kuma ƙungiyarsa Juventus, da ke son aƙalla fam miliyan 25 dindi ta ƙi sallamawa (Gazzetta dello Sport)