Ten Hag bai ji daɗi ba da Rosenborg ta doke Man United

Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta yi rashin nasara da ci 1-0 a hannun Rosenborg a wasan sada zumunta ranar Litinin a Norway.

An fara wasan da Marcus Rashford da Casemiro da Mason Mount da Jonny Evans da kuma Aaron Wan Bissaka, amma suka je hutu ba ci a karawar.

Daga nan United ta saka matasan ƴan wasan a zagaye na biyu da Rosenborg ta ci 1-0 a wasan na atisayen tunkarar kakar 2024/2025.

Erik ten Hag bai yadda da wani korafi ba ganin cewar shi ne wasan farko da United ta buga a shirin ganin ta taka rawar gani a kakar da za a fara ta bana.

To sai dai an jinjina wa matashin mai tsaron ragar United, Noah Holm, wanda ya hana ƙwallo biyar shiga raga.

Wannan shi ne wasan farko da Ten Hag ya ja ragamar ƙungiyar Old Trafford, tun bayan da ya tsawaita ƙwantiragin kaka ɗaya a United.

''Bai kamata mu yi rashin nasara ba, duk da wasan sada zumunta ne, ya kamata Manchester United ta ci karawar, idan har ba za ka yi nasara ba to kada a doke ka.

''Ba mu taka rawar gani ba, mu Manchester United ne ya kamata ƙwazon mu ya wuce haka.''