Rikicin Ukraine da Rasha: UEFA za ta dauke wasan karshe na Zakarun Turai daga St Petersburg

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Kwallon Kafa ta Turai ta tabbatar da cewa za ta dauke wasan karshe na gasar Zakarun Turai daga birnin St Petersburg, biyo bayan kutsawa Ukraine da Rasha ta yi.
A ranar Juma'a ne UEFA za ta yi wani zaman gaggawa na masu ruwa da tsaki don daukar mataki na gaba kan batun.
Da safiyar Alhamis ne Shugaban Rasha Vladimir Putin ya kaddamar da hari kan Ukraine mai makwabtaka.
Itama Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya FIFA za ta gana da wakilan Rasha da na Ukraine kan wasannin neman gurbin zuwa gasar Qatar 2022 da za su buga cikin watan Maris.
An tsara cewa Rasha za ta buga da Poland a ranar 24 ga watan Maris, yayin da Scotland za ta karbi bakuncin Ukraine duka a rana daya.
Kazalika a karshen mako ne aka shirya dawowa hutu na wasannin cikin gida a Ukraine, to amma ga alama da wahala hakan ta yiyu.
Dama UEFA ta kai wasan karshe na gasar Zakarun Turai a filin Gazprom Arena da ke birnin St Petersburg a ranar 28 ga watan Mayu, to amma yanzu ta fahimci cewa ba abu ne mai yiyuwa ba.
Shugaban UEFA Aleksander Ceferin ya kira taron gaggawa ranar Juma'a don tabbatar da matakin dauke wasan daga Rashar.

Asalin hoton, Reuters
Matakin na nufin kaka uku kenan a jere UEFA na sauya inda za a buga wasan karshe cikin kankanin lokaci bisa wasu dalilai.
To amma wasan Europa League zagaye na biyu da Zenit St Petersburg za ta je gidan Real Betis yau Alhamis na nan daram.
A cewar masu sharhi UEFA za ta so Real Betis ta cire Zenit St Petersburg a yau, don matsawar ta fito akwai yiyuwar cire ta daga gasar, ko kuma akalla a tilasta mata buga wasa a wata kasa daban.
A zagayen farko Zenit ta yi rashin nasara a gida 3-2, kuma a yau za ta nemi samun nasara ne a filin Benito Villamarin da ke Seville.











