Champions League: Elanga ya kwaci United a Madrid, Benfica da Ajax sun tashi 2-2

Elanga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An raba maki tsakanin Manchester United da Atletico Madrid a wasan Zakarun Turai zagayen kungiyoyi 16.

Tun a mintunan farko ne mai masaukin bakin ta bude raga ta hannun Joao Felix, kuma sai a minti na 80 Anthony Elanga ya farke wa bakin da hakan yasa aka tashi 1-1 a filin Wanda Metropolitano.

A cewar mai horar da United Ralf Ragnick bai ji dadin yadda yan wasansa suka gaza tabuka komai ba a minti 45 na farko.

To amma ya ce ya ji dadin yadda suka zaburo bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Ya kuma jinjina wa matashin dan wasansu Anthony Elanga da ya kwace su, da kuma rawar da Victor Lindelof ya buga a baya.

Ya kara da cewa yana da kwarin gwuiwa wasan da za su buga wa Atletico Madrid a Old Trafford gaban yan kallo 75,000 zai fi na yau.

Elanga

Asalin hoton, Getty Images

Sai a ranar 15 ga watan Maris za a raba gardama a Old Trafford da ke birnin Manchester.

A daya wasan na ranar Laraba an tashi 2-2 tsakanin Benfica da Ajax a Lisbon.

Bakin ne suka fara ci ta hannun Dusan Tadic a minti na 18, amma an farke bayan da Sebastian Haller ya ci gida.

To amma dan wasan gaban na Ajax ne ya sake ci wa kungiyarsa ta biyu, kafin a minti na 72 Roman Yaremchuk ya mayar da ita 2-2.

Sakamakon na nufin za a kwashi yan kallo a Amsterdam ranar 15 ga Maris.