Rikicin Ukraine: Uefa na duba yiyuwar sauya inda za a buga wasan karshe na Zakarun Turai

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Turai Uefa na duba yiwuwar sauya wurin da za a buga wasan ƙarshe na gasar Zakarun Turai ta Champions League daga birnin St Petersburg sakamakon fargaba da ake da ita kan rikicin Ukraine da Rasha.
Rasha ta tura dakaru zuwa yankuna biyu na Ukraine da suka ayyana 'yancin kansu kuma ana fargabar Rashar za ta afka wa Ukraine ɗin.
Wannan dalilin ne ya sa ake ganin Uefa ba za ta bari a buga wasan ƙarshen ba a ƙasar.
Da yake magana ranar Talata, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce "ba zai yiwu a buga wasan ƙwallo ba a ƙasar da ke afka wa ƙasashe masu 'yanci".
A gefe guda kuma, tsohon Ministan Wasanni na Birtaniya Tracey Crouch ya faɗa wa BBC cewa ya kamata Uefa ta ɗauke wasan daga Rasha "da gaggawa".
BBC ta fahimci cewa ba za a sauya ranar da za a buga wasan ba a 28 ga watan Mayun 2022 duk da cewa ana sa ran Uefa za ta yanke hukunci bayan tattaunawa kan wani filin wasan.







