Man United ta ci Brighton 2-0, ta dawo ta hudu a Premier

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallon farko bayan an dawo hutun rabin lokaci, a wasan farko da United taci cikin wasanni hudu.
Jim kadan bayan haka mai tsaron bayan Brighton Lewis Dunk ya karbi jan kati.
Kuma kamar za su rama a minti karshe United ta kai kora ta hannun Bruno Fernandez, wanda ya gar gola kafin saka kwallon ta biyu a mintin karshe.
Sai a wannan karon Ronaldo ya ci kwallo a wasanni shida da ya buga wa United.

Asalin hoton, Getty Images
Dama kwanton wasa ne da United ke burin hawa na hudu dashi, bayan kasa cin wasanni uku a jere.
Da sakamaakon United ta sauko da West Ham zuwa na biyar da maki 43.
A ranar lahadi United za ta nika gari zuwa Elland road don karawa da Leeds United.







