Novak Djokovic: Dan wasan tennis na duniya ba zai yi rigakafin korona

Asalin hoton, QUALITY SPORT IMAGES
Dan wasan tennis na daya a duniya Novak Djokovic ya ce ya gwammace ma ya rasa kofuna a nan gaba da ya yadda a yi masa rigakafin cutar korona.
A hira ta musamman da BBC, ya ce a shirye yake da yaki halartar gasar French Open matsawar aka bukaci sai ya yi allurar rigakafin.
A watan da ya gabata ne aka soke wa dan wasan da ya lashe manyan kofunan Grand Slams 20 takardun izinin shiga Australiya, saboda rashin sanin ainihin halin da yake ciki game da rigakafin.
Dan kasar Sabiya din ya ce halin da ya shiga lokacin da hukumomin Australiya suka tsare shi ba mai dadi bane.
Djokovic ya kuma ce ya ki magana da yan jarida a lokacin duk da ya so ya yi hakan, saboda ya martaba dokokin kasar da kuma gasar ta Australian Open.
A cewarsa ya yadda da yancinsa na ya amince ko akasin haka game da yi masa rigakafi, amma kuma baya goyon bayan kungiyoyin da ke adawa da yin rigakafin.
Djokovic ya ce kafin ya tafi Australiya sai da ya samu takarda daga likitoci da ta nuna cewa ya warke daga cutar korona, don haka zai iya shiga kasar don buga gasar Australian Open.
To sai dai ministar cikin gida Alex Hawke ta soke takarunsa na bisa, bisa dalilin cewa bashi damar shiga zai haifar da tashin-tashina da zanga-zanga kan batun.
''Ni ban taba adawa da rigakafi ba don an yi mini da ina karami. Amma kuma ina goyon bayan yancin zabar abunda za a dura mani cikin jikina.'' In ji Djokovic.











