Hotunan halin da ake ciki game da batun juyin mulki a Sudan
An wallafa
Sojojin Sudan sun kifar da gwamnatin farar hula, sannan suka kama shugabannin siyasa, kana shuka ayyana dokar ta-baci.
Janar Abdel Fattah Burhan, wanda ya jagoranci gwamnatin hadaka da farar hula, ya dora alhakin abin da ke faruwa kan rikicin siyasa na cikin gida.
Gajerin hotunan abubuwan da ke faruwa a kasar ta Sudan:

Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, An shafe kwanaki ana zanga zangar goyon baya da kuma adawa da sojoji a Khartoum, babban birnin Sudan
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Masu bore kenan kan titi bayan sun kona tayoyi tare da rufe hanyoyi
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Ana fargabar za a sake shiga sabon kazamin rikici tsakanin sojoji da fararen hula kamar yadda aka gani a baya a Sudan
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, An samu rahotannin girke sojoji a birnin Khartoum babban birnin na Sudan
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Mutane da dama sun yi murna bayan kifar da gwamnatin Omar Al-Bashir sai ga wani sabon rikici ya kunno kai
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Firaminista Abdalla Hamdouk da aƙalla ministoci huɗu na cikin waɗanda sojoji da ba a tantance ba suka kama