APC: Gwamnonin jam'iyyar sun yanke shawara kan shugabancin Mai Mala Buni

Gwamnonin jihohin Najeriya da aka zaba a inuwar jam'iyyar APC mai mulki sun kada kuri'ar amincewa da shugabancin riko na jam'iyyar na kasa, karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.
Dama dai ana dai takadamma kan sahihancin shugabancin nasa inda wasu kusoshin jam'iyyar ke bukatar ya sauka saboda zamansa shugaba ya saba doka a cewarsu, kuma hakan ka iya yi wa jam'iyyar illa nan gaba a zabuka na gama-gari.
Amma gwamnonin sun ce ba su hangen akwai matsala tafe domin doka ba ta hana gwamna Mai Mala damar shugabantar jam'iyya a matakin kasa ba.
Shugaban kungiyar gwamnonin na APC, kuma Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya shaida wa BBC cewa sun kara ji bayani daga masana shari'a kan wani hukuncin kotun koli kan batun gwamnan jiha ya kasance shugaban jam'iyya.
Bisa wannan dalili ne suka amince cewa sun amince da shugabancin rikon kwarya na Mai Mala Buni da sauran mambobin kwamitin da ya ke jagoranta.
A cewar Gwamna Bagudu, gwamnononin na APC sun gamsu da kamun kudayin shugaban kwamitin rikon kwaryar musamman saboda ''ci gaban da aka samu a jam'iyyarmu karkashin jagorancin Mai Mala Buni da duka wadanda suke aiki tare da shi.''
Ga alama yana nuni ne da yadda wasu 'yan manyan 'yan jam'iyyar hamayya suka koma cikin jam'iyyar. Wannan dambarwa na faruwa ne yayin da jam'iyyar ke gudanar da zaben shuwagabanninta a matakai daban-daban a fadin kasar.
Shin matakin gwamnonin APC zai ceci jam'iyyar ta APC daga wutar rigimar?
Masu sharhi na cewa babu tabbas kan ko wannan mataki na gwamnonin jam'iyyar APC zai kawo karshen dambarwar shugabancin jam'iyyar mai mulki.
Wasu ma na ganin ka iya harzuka wasu 'ya'yan jam'iyyar da basu gamsu da kasancewar Mai Mala Buni a matsayin shugaba ba. Irin wannan rigimar ta cikin gida ce ta yi sanadi tsofoffin shuwagabannin jam'iyyar Adams Oshiomole da kuma John Oyegun suka rasa mukaman nasu a can baya.
To amma gwamnan jihar Kebbi Bagudu ya ce suna da kwarin gwiwa kan tasirin matakin nasu wajen samar da natsuwa a jam'iyyar. A cewarsa ''babu wata matsala.''
Duka wannan na faruwa ne yayin da Najeriya ke ci tunkarar manyan zabuka na 2023 lokacin da wa'adin mulkin shugaba Muhammadu Buhari zai kare, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Wasu na ganin wannan rigima ta shugabanci a cikin gida, ka iya zama zakaran gwajin dafi ga dorewar hadin kai na jam'iyyar ta APC da kuma tasirinta a siyasar Najeriya.
Labarai masu alaka:
Ita ma jam'iyyar hamayya ta PDP na da tata rigimar
Yayin da jam'iyyar APC mai mulki ke kokarin dinke barakar dake cikinta, ita ma babbar jam'iyyar hamayya ta ta PDP na fuskantar babbar baraka kan shugabancinta na kasa baki daya.
Wasu manyan 'yan jam'iyyar na matsa lamba kan shugabanta Uche Secondus da ya saiuka daga mukaminsa ko kuma a cire shi domin ba su gamsu da kamun ludayinsa. A ranar Litinin su ma gwamnonin jam'iyyar PDP sun yi taro kan barakar dake cikin jam'iyyar.

Asalin hoton, PDP
To amma ba su bayyana takamaimai matakin da suka cimma ba. Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar, ya shaida wa BBC cewa ba su kai matakin da zasu bayyana abin da suka cimma a taron ba tukuna.
Wasu na kallon wannan lamari a matsayin wata babbar alama dake nuna cewa akwai sauran rina a kaba a jam'iyyar. Ita ma jam'iyyar ta PDP ana ganin rikicin shugabancin nata na da nasaba da zaben shugaban kasa na 2023 musamman batun yankin da ya kamata dan'takararta ya fito.
Jam'iyyar ta mulki Najeriya tsawon shekara 16 kafin jam'iyyar APC ta doke ta a 2015. Wasu na kallon rigingimun cikin gida na manyan jam'iyyun biyu watom APC da PDP a matsayin wata manuniya ga yadda zabukan kasar na gaba zasu kasance baki daya.









