Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin ‘yan kwallo: Makomar Alli, Laborde, Garcia, Sanson da Depay
Dan wasan Tottenham da Ingila Dele Alli, mai shekara 24, yana "kokarin" tafiya Paris St-Germain sai dai ana samun tangarda game da yunkurin nasa. (Italian journalist Fabrizio Romano, on Twitter)
West Ham United suna duba yiwuwar zawarcin dan wasan Faransa Gaetan Laborde mai shekara 26, wanda ke murza leda Montpellier. (Telegraph - subscription required)
Shugaban riko na Barcelona Carles Tusquets yan shawarci 'yan takarar shugabancin birnin su uku su dauko dan wasan Manchester City da Sifaniya Eric Garcia, mai shekara 20,a kan 8m euros (£7.1m), amma da wahala su dauki shawarar tasa domin bakinsu bai zo daya kan batun ba. (Marca)
Dan wasan Netherlands Memphis Depay, mai shekara 26, ya ce shi da abokinsa da murza leda a Lyon Houssem Aouar, mai shekara 22, suna son tafiya "daya daga cikin manyan kungiyoyi uku na duniya". Ana hasashen Depay zai tafi Barcelona, yayin da shi kuma Aouar ake rade radin zai tafi Arsenal. (Canal+)
Kocin Fulham Scott Parker ya ce yana son dauko 'yan wasa kuma yana neman kungiyar ta kammala cinikin 'yan kwallon watan Janairu da wuri. (Evening Standard)
Kocin Marseille Andre Villas-Boas ya tabbatar da cewa kungiyoyin Ingila na zawarcin dan wasan Faransa Morgan Sanson, inda ake hasashen dan wasan mai shekara 26 zai tafi Arsenal, Aston Villa, Tottenham ko West Ham. (Mail)
Daraktan Inter Milan Beppe Marotta ya ce kungiyar tana kudin da za ta sayi 'yan wasan amma duk da haka ba za ta yi cinikin 'yan kwallo a watan Janairun ba. (Sky Sport Italia, in Italian)
Kocin Hull City Grant McCann ya ce ba za su sayar da dan wasan Ingila Keane Lewis-Potter ba, duk da rahotannin da ke cewa an fuskanci matsala game da sabunta kwangilar dan wasan. (Yorkshire Post)