Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ana hutu a gasar La Liga saboda Spanish Super Cup
Ranar Talata za a ci gaba da wasannin La Liga a Spaniya, karawar mako na 19 da za a yi karawa uku a ranar.
Za a buga wasan karshe a Spanish Super Cup tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao a filin wasa na Sevilla.
Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga, ita kuwa Bilbao tana ta 12 a kasan teburi.
Atletico Madrid wadda keda kwantan wasa biyu, ita ce kan gaba a teburi da maki 41, sai Real Madrid ta biyu mai maki 37.
Kawo yanzu an buga wasa 177, amma wasu kungiyoyin suna da kwantan wasa da aka kai fafatawar mako na 18, an kuma ci kwallo 427, Barcelona ce kan gaba mai 37 a raga.
Lionel Messi kyaftin din Barcelona shi ne kan gaba a cin kwallaye a gasar Spaniya mai 11 a raga, Gerard Moreno dan wasan Villarreal da ya zura 10 a raga, sai Iago Aspas na Celta Vigo da kuma Luis Suarez na Atletico Madrid da kowanne keda tara-tara a raga.
Kawo yanzu wasan da aka ci kwallaye da yawa a gida shi ne wanda Atletico ta doke Granada da ci 6-1 ranar 27 ga watan Satumbar 2020.
Fafatawar da kungiyar waje ta je ta ci kwallaye da yawa shi ne wanda Villareal ta je ta doke Celta Vigo 4-0 ranar 8 ga watan Janairun 2021 da wanda Barcelona ta je gidan Granada ta yi nasara da ci 4-0 ranar 9 ga watan Janairun 2021.
Wasannin mako na 19 za a fafata a gasar La Liga.
Ranar Talata 19 ga watan Janairu
Real Valladolid da Elche
Cadiz da Levante
Deportivo Alaves da Sevilla
Ranar Laraba 20 ga watan Janairu
Getafe da Huesca
Real Betis da Celta Vigo
Villarreal da Granada
Ranar Alhamis 21 ga watan Janairu
Valencia da Osasuna
Eibar da Atletico Madrid
Levante da Real Valladolid
Huesca da Villarreal