Trump zai koma yakin neman zabe duk da babu tabbacin ya warke

Asalin hoton, Getty Images
Nan gaba kadan ne Shugaba Donald Trump na Amurka, ke shirin komawa domin ci gaba da yakin neman zabe, kwana 11 bayan da aka gano yana dauke da cutar korona.
Mista Trump na shirin gudanar da wani jawabi a Florida wanda ya ce a nan ne zai gudanar da babban gangami bayan da yace a yanzu ya samu kariya daga cutar.
Tunda farko dai sai da babban jami'in masu yaki da cutar korona Anthony Fauci ya ce an yanki wani bangare na kalamansa ba bisa ka'ida ba wajen tallata shugaba Trump.
Babban jami'in ya yi kalaman ne bayan da aka sallami Mr Trump daga asibiti bayan ya kwanata domin magani sakamakon kamuwa da cutar korona da ya yi.
Daga cikin inda aka yanka har da inda Dakta Fauci ya yi bayani a kan cewa yana samun sauki daga cutar.
Kodayake Dakta Fauci ya ce sam ba haka batun yake ba, domin shi inda aka dauka a jawabin nasa har aka yi amfani dashi bayani ne da ya yi tun watannin baya da suka shude a lokacin da ya ke bayani a kan irin kokari da jajircewar da ma'aikatan lafiya ke yi wajen yaki da cutar.
Kazalika an yi amfani da wasu daga cikin sakonnin da Mr Trump din ya wallafa a shafinsa na twitter cewa likitocin fadar gwamnatinsa sun bashi tabbacin cewa ya samu kariya daga wannan cutar.abinda twitter din ya ce ya saba ka'idojinsa wajen yada zancen da ba haka yake ba musamman wanda ya ke da alaka da cutar korona.
Dr Fauci, ya bayyana cewa a tsawon kusan shekaru 50 da ya shafe yana aiki, bai taba fitowa ya goyi bayan wani dan takarar siyasa ba.
An dai samu ma'aikatan fadar gwamnatin Amurkan 34 da suka kamu da cutar korona a 'yan kwanakin nan a cewar kafofin watsa labarai a Amurka.











