Coronavirus: Abin da zai faru idan rashin lafiyar Trump ta yi tsanani

Trump and Pence

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump tare da mataimakinsa Pence yayin da aka kaddamar da su a matsayin 'yan takarar jam'iyyar Republican a watan Agusta
    • Marubuci, Daga Tawagar Bin Diddigi ta Reality Check
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • An wallafa

Ana makonni gabanin zaben shugaban kasar Amurka, sai ga Mista Donald Trump ya kamu da cutar korona.

Wannan lamarin ya haifar da jerin tambayoyi game da abin da zai iya faruwa a kasar.

Wadanne gangamin siyasa shugaban zai fasa halarta?

Ana bukatar shugaba Trump ya killace kansa na kwana 10 daga ranar da ya karbi sakamakonsa na cewa ya harbu da cutar. Saboda haka yana iya halartar muhawara ta gaba da aka shirya yi ranar 15 ga watan Oktoba.

Amma an soke wani gangami da aka shirya yi a jihar Florida. A madadin haka shugaban zai buga waya daga Fadar White House ga dattawa irinsa masu raunin kiwon lafiya.

Akwai kuma wasu tarukan na siyasa da aka shirya gudanarwa, amma babu makawa tilas a soke su ko a ɗage su zuwa wani lokaci.

Wane dalili ne zai sa a jinkirta gudanar da zaben?

Killace kansa da shugaban ya yi zai yi tasiri kan damar da yake da ita ta yin kamfe.

Saboda haka ake tambayar ko za a iya jinkirta zaben, kuma ya hakan zai kasance?

A karkashin dokar Amurka, a kan yi zabe ne a ranar Talatar da ke bin Litinin ta farko a watan Nuwamba, a kowace shekara hudu - saboda haka a bana ranar 3 ga watan Nuwamba ke nan.

Sauya wannan ranar na hannun 'yan majalisar kasar ne ba shugaban kasa ba.

Saboda haka sai mafi rinjayen 'yan majalisun wakilai da na dattawa sun kada kuri'ar yin haka kafin a iya sauya ranar zaben. Ko shakka babu samun faruwa wannan matakin zai yi wuya ganin cewa tilas dokar ta bi ta hannun majalisar wakilai wadda jam'iyyar Democrat ke da gagarumin rinjaye a cikinta.

President Trump at first debate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya tafi da takunkumi wurin muhawararsa da Joe Biden amma bai sanya shi ba

Sannan ko an yi sauyin, tsarin mulkin Amurka ya tanadi cewa mulkin shugaban kasar na tsawon shekara hudu ne kawai.

Saboda haka wa'adin mulkin Mista Trump zai kare ranar 20 ga watan Janairu 2021.

Shi ma yin sauyi ga ranar da wa'adin zai kare na bukatar amincewar majalisun kasar a matakin tarayya da matakin jihohi - wanda ba abu ne mai yiwuwa ba.

Me zai faru idan Shugaba Trump ya zama ba ya iya yin aikinsa

A halin da ake ciki an ce shugaban na da alamun cutar ne kawai, amma idan rashin lafiyarsa ta sa ba ya iya yin aikinsa na shugaban kasa, ga abin da tsarin mulkin Amurka ya ce a yi:

Gyaran da aka yi wa tsarin mulkin kasar na 25 ya ce shugaban kasa na iya mika mulkinsa ga mataimakinsa, wanda ke nufin Mike Pence zai zama mataimakin shugaban kasa ke nan. Amma da zarar ya murmure, Mista Trump na iya karbar mukaminsa.

Wannan ya taba faruwa karkashin mulkin Ronald Reagan da George W Bush.

Trump and Marine One

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Trump ya shiga jirginsa na helikwafta tare da Hope Hicks, wata mata mai yi ma sa hidima ranar Laraba. JIm kadan sai ya kamu da cutar korona.

Amma idan shugaban ya shiga halin da ba zai iya mika mulki da kansa ba, sai ministocinsa da mataimakin shugaban kasa su taru su ayyana haka, kuma su mika wa mataimakin nasa mulki.

Idan kuma shi kansa Mista Pence ya sami kansa a irin wannan halin, to a karkashin tsarin mulkin, sai shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi - wadda 'yar jam'iyyar Democrat ce ta zama shugaban kasa.

Idan ita ma ta kasa yin haka sai a mika mulkin ga wani babban sanata daga jam'iyyar Republican wanda a yanzu sunansa Charles E Grassley, wanda ya ke da shekara 87 da haihuwa.

Pence wears mask

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence na iya gadan mukamin mista trump idan ya shiga wani hali