Coronavirus ta kama mutum 92 cikin sa'o'i 24 a Kano

Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, @GovUmarGanduje

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Cutar korona tana ci gaba da mamaya a jihar Kano da ke arewacin Najeriya inda sabbin alkaluman da hukumomi suka fitar a daren Juma'a suka nuna cewa karin mutum 92 sun harbu da cutar cikin sa'a 24.

Alkaluman da ma'aikatar lafiya ta Kano ta fitar sun ce yanzu adadin masu cutar korona a jihar ya kai 311.

Sannan akwai karin mutum uku da suka mutu wanda ya kawo adadin mamata zuwa mutum 8, kuma har yanzu babu mutum ko guda da ya warke daga cutar.

Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC, ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1006.

Kashi 71 cikin 100 na wadanda aka samu dauke da cutar sun fito ne daga jihohin Legas da Kano da kuma birnin Tarayya Abuja.

Wadannan alkaluman da hukumar NCDC ta fitar a daren Juma'a na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke kara yaduwa a cikin gaggawa a jihar Kano.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

A baya-bayan nan an rinka samun mace-mace masu yawa tsakanin jama'ar jihar ta Kano, sai dai gwamnatin jihar ta ce babu alakar karuwar mace-macen da cutar korona.

Amma wasu likitoci masu zaman kansu sun alakanta mace-macen da cutar ta korona.

Yanayin da jihar Kano ta tsinci kanta na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke bayyana fargabar watakila a samu koma-baya a yakin da ake yi da annobar korona a Najeriya saboda rashin kayan aiki.

Likitocin dai su na kukan rashin kayan kariya, lamarin da suka ce yana jefa su cikin hadarin harbuwa da cutar korona.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

A farkon makon nan ne dai gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi zargin cewa an watsar da jiharsa a yakin da gwamnatin Tarayya ke yi da wannan anno

Wannan dalilin ne ya sanya shugaban kasar ya sanar da dokar hana fita ta mako biyu da kuma tura wani ayarin manyan jami'an kiwon lafiya zuwa jihar domin gudanar da bincike da kuma dakile matsalolin da ke fuskata.

Yanzu dai akwai mutane sama da dubu biyu da ke dauke da cutar korona a Najeriya, cikinsu 351 sun warke yayin da 68 suka rasa rayukansu.