China: Coronavirus ta fara raguwa kwana uku a jere

@

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An samu raguwar masu kamuwa da cutar coronavirus a kasar Chana.

Hukumomin kasar sun ce kwana uku a jere ke nan da yaduwar kwayar cutar ke kara raguwa a kasar.

Gwamnatin kasar ta sanar cewa mutum 2,009 ne suka kamu da cutar yayin da wasu mutum 142 suka rasu, a ranar Lahahi 16 ga watan Fabrairun 2020.

An samu karuwar wadanda ke kamuwa da cutar a cikin makon jiya bayan hukumomi sun sauya tsarin kidayar masu kamuwa da cutar. Daga baya an yi ta samun raguwar masu dauke da ita.

Ya zuwa yanzu mutum 68,000 ne suka kamu da coronavirus a China, yayin da ta yi ajalin mutum 1,665.

Mutum 500 na dauke da kwayar cutar a kasashe kusan 30 inda mutum hudu suka mutu ta sanadiyyar cutar a Faransa da Japan da Filifins da Hong Kong.

Jami'in hukumar lafiyar China, Mi Feng, ya ce matakan da suke dauka na dakile yaduwar cutar sun fara yi tasiri sosai.

A wasu wuraren kuma:

  • Yawan masu dauke da cutar a jirgin ruwan alfarma da aka killace a Japan ya karu zuwa 355. Amurka da Canada na tura jirage domin kwashe 'yan kasarsu.
  • Wani mai yawon bude ido dan asalin kasar Chana ya rasu a Faransa - wadda ita ce mutuwa ta farko ta coronavirus a wajen nahiyar Asiya.
  • A kasar Kambodiya an gano wata 'yar Amurka mai shekara 83 na dauke da coronavirus bayan saukowar ta daga wani jirgin ruwa da wasu kasashe suka hana shi tsayawa a tashoshinsu.
  • A Birtaniya kuma an sallami mutum takwas daga cikin mutum tara da aka kwantar a asibiti saboda cutar.
  • Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yaba wa China bisa matakan da ta dauka wajen dakile yaduwar coronavirus.