'Na koma ba da hannu a titi bayan dana ya mutu a hatsarin mota'

Monica Dongban-Mensem ta na bayar da hannu a titi
    • Marubuci, Daga Dooshima Abu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin, Abuja
  • An wallafa

A lokacin da ba ta aikin komai, Justice Monica Dongban- Mensem, ta kan je titi ta rinka bayar da hannu a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, shekaru takwas bayan an kade danta da mota ya mutu.

A ranar da wakiliyar BBC ta hadu da ita, ta ganta tana cikin shudayen kaya tana bayar da hannu a kan titi.

Justice Monica, tana kusa da sha tale-talen Berger ne wanda ke a tsakiyar Abuja.

A wajen akwai cunkoson ababen hawa da mutane, motocin da suke a wajen sun tsaya suna jiranta ta ba su hannu domin su wuce.

Idan ka ganta za ka san lalle aikin da gaske take.

"Mafi yawancin 'yan Najeriya dai ba su da hakuri, kuma ana iya gani ma ko a tukinsu," in ji Justice Dongban-Mensem.

Dongban-Mensem campaigning
Bayanan hoto, Monica Dongban-Mensem, a tsakiya a lokacin da ta karbi takardar shaidar kammala horon da ta samu na bayar da hannu

Ba ta san wanda ya kade danta har ya mutu ba, amma kuma tana so ta kawo karshen masu tukin gangancin da suke kade mutane suna gudu.

Da farko sai ta fara zuwa wuraren da motocin haya ke tsayawa tana tattaunawa da direbobi a kan aikin jami'in kiyaye afkuwar hadura na Najeriya.

Abin da ta gano a lokacin ya kadata sosai.

Mafi yawancin direbobin da ke tuka mota ba su da wani kwakkwaran horo da kuma sanin ka'idojin hanya da na tuki.

Ba mamaki irin wannan sakacin ne ya janyo mutuwar danta, abin da kuma ya sa ta kuduri aniyar kawo sauyi a kan hakan.

Justice Monica Dongban- Mensem, 'yar kimanin shekara 62 ce, ta kafa wata kungiya da ta sanya wa sunan danta -Kwapda'as Road Safety Demand, domin a rinka horar da masu tuka mota a kan yadda za su rinka kiyayewa, sannan kuma tana shirin samar da makaranta koyon tuki ga direbobin motocin haya.

Accidents and road deaths in Nigeria. Showing data from 2012 - 2018. Chart showing accidents and road deaths in Nigeria between 2015-2019. .
Presentational white space

Ba a nan kawai ta tsaya ba, Justice Dongban-Mensem, na son ta rinka bayar da hannu da kanta.

Bayan ta shafe wasu satuka tana karbar horo a hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya, ta samu shaidar cewa za ta iya bayar da hannu a tituna.

A lokacin, shekara biyar da mutuwar danta, anan ta ziyarci wajen da aka kade danta a tsakiyar birnin Jos na jihar Filato.

Ta ce " Burina shi ne na samu wanda zai fada mini ko kwatanta mini yadda dana ya mutu".

To amma da zarar ta je wajen, sai dai ta tafi a cikin bacin rai da takaici.

Cunkoson ababen hawa a wata babbar hanya a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mafi yawancin manyan titunan biranen Najeriya na fama da cunkoson ababen hawa

Mahadar Miners da ke unguwar Tundun Wada a birnin Jos, na daya daga cikin mahadar da ke da cunkoson ababen hawa saboda ta hada da manyan wuraren kasuwanci a jihar Filato.

Ta ce hanya irin wannan na da matukar hadari wajen ketara ta, saboda ana yawan samun hadura, kamar abin da ya samu dana Kwapda'as Dongban, dan kimanin shekara 32 a shekarar 2011.

Justice Monica, ta ce "Ni a ganina hanya irin wannan tana da matukar hadari, kuma ana kashe mutane da dama a kanta, amma kuma babu wata gwamnati da ta yi kokari kawo gyara a tsarin titin".

To sai dai kuma mahukunta a Jos, sun shaida wa BBC cewa, suna gyara hanyoyin da suka lalace, sannan kuma sukan jajantawa wadanda suka rasa wani nasu.

Mutane a wajen da aka kade danta sun shaida mata cewa, sun ga danta kwance a kan titi, kuma ba za su iya taimaka masa ba.

Monica Dongban-Mensem
BBC
I gave up sleep, hoping that my son will walk through the door and give me a big hug"
Monica Dongban-Mensem
Presentational white space

Justice Dongban-Mensem, ta fada a cikin bacin rai cewa: "A lokacin da aka kade dana, kafafunsa biyu sun karye, sannan wadanda ke wajen sun dauke kansu a yayin da dana ke kukan ciwon da yake ji, ya rinka zubar da jini".

Ta ce "Ya mutu ne saboda jinin da ya zubar, na tabbata da an yi maza an kai shi asibiti da wuri da ya rayu".

Dan nata bai jima da kammala karatun jami'a ba a Jami'ar Jos, ya kuma je birnin Jos din domin ya karbi takardar shaidar kammala karatunsa a lokacin ne aka kade shi ya mutu.

Ta ce "Dana na son zama lauya ne, amma kuma daga karshe ya yi mutuwar ban takaici".

A cewar hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Najeriya, an dan samu raguwar hadura a 2013, amma kuma tun daga wannan shekara, mutane 5000 ko 6000 na mutuwa a kowacce a shekara sakamakon hadarin mota.

Mafi yawancin haduran da ake yi direbobi ne ke janyo su wadanda ba su da lasisin tuki in ji mahukunta.

A misali, a watan Mayun 2019, mutane fiye da dubu 60 a Legas na tuki ba tare da lasisin tuki ba.

Sannan kuma, babu rumbun adana bayanai na motocin da suke da rijista ko kuma kamarori da ake sanyawa a kan tituna wadanda za su iya daukar duk wani abin da ya faru.

Abin da ke sa a sha wuya wajen gano irin direbobin da ke kade mutane suna gudu kamar yadda aka yi wa dan Justice Dongban- Mensem.

Ambulance on Nigerian road
BBC
Road safety in Nigeria

  • 200 millionpeople

  • 12.5 millionvehicles

  • 5,181deaths on the roads in 2018

  • 965accredited driving schools

Source: FRSC
Presentational white space

Da ana kama irin direbobin da suke kade mutane suna gudu ana kuma yanke musu hukuncin da ya dace da su, da an samu raguwar masu aikata irin haka.

To sai dai Justice Dongban-Mensem ,ta ce kamata ya yi idan aka kama direban da ya kade mutum ya gudu, to a yanke masa hukuncin daurin rai da rai, sannan kuma a rinka ba wa iyalan wadanda aka kade suka mutu diyya.

To amma duk da haka, yin hakan ba zai gusar wa iyalan babban rashin da suka yi ba, inji Justice Dongban-Mensem.

Presentational grey line
Presentational grey line

Ta ce "Na daina barci, ina fatan ganin dana ya shigo gida ya rungume ni".

Na kan kuma bar kwanon abinci guda a kullum, ina ganin dana zai dawo gida da yunwa ya ci".

Ba ta son wata uwa ta shiga halin da ta samu kanta a ciki.