Makami mai linzami ya kashe sojojin Yemen 80

Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wani harin makami mai linzami ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 80 a wani sansanin horas da sojoji da ke kasar Yemen.

Harin ya raunata gwamman sojoji a sansanin da ke tsakiyar lardin Marib a ranar Asabar, kamar yadda jami'ai suka tabbatar.

Harin dai ya faru ne yayin da jama'a ke niyyar yin sallah a sansanin wanda yake da nisan kilomita 170 daga Sanaa babban birnin kasar.

Gwamnatin Yemen din dai ta dora alhakin harin kan 'yan tawayen Houthi duk da cewa babu wata kungiya da ta fito fili ta dauki nauyin kai harin.

Jami'an kasar dai sun bayyana cewa suna ganin za a kara samun wadanda suka mutu cikin wadanda ke da raunuka a halin yanzu.

A wata sanarwa da Shugaban kasar Abdrabbuh Mansour ya fitar ta kamfanin dillancin labarai na Saba, ya yi Allah waddai da harin.

Ya bayyana cewa ''harin ya tabbatar mana da cewa 'yan tawayen Houthi ba su da bukatar zaman lafiya''.

A watan Agustan bara, 'yan tawayen Houthi sun kai harin makami mai linzami ga wani jerin sojojin kasar ta Yemen masu fareti wanda harin ya yi sanadiyar mutuwar sojoji 32 a birnin Aden.

Rikicin Yemen ya kara ta'azzara ne bayan da 'yan tawayen Houthi suka kwace ikon akasarin garuruwan da ke yammacin kasar inda suka tilasta wa Shugaba Hadi ya bar kasar.