MDD ta nemi a kawo karshen 'kashe-kashe' a Iraki

Reuters

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a kawo karshen abin da ta kira ''kashe-kashe'' a Iraki a daidai lokacin da mutanen da aka kashe sakamakon zanga-zangar suka kusan 100.

Masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar sun bayyana cewa suna wannan zanga-zangar ne sakamakon rashin aikin yi da cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu.

Jeanine Hennis-Plasschaert, wacce ita ce Shugabar shirin bayar da agaji ta MDD a Iraki ta ce ''cikin kwanaki biyar an mutu dayawa kuma an samu raunuka: dole a dakata.''

Ta bayyana cewa yakamata a yi hukunci ga wadanda suka yi sanadiyar mutuwar gwamman mutane.

A ranar Asabar, jami'an tsaro sun tarwatsa wata zanga-zanga da aka yi a gabashin kasar.

A sabuwar arangamar da aka yi tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zangar, an shaida cewa mutum biyar ne suka rasa rayukansu a babban birnin kasar.

An zargi jami'an tsaron kasar da sake amfani da harsasai da kuma hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

Wannan shi ne sabon rikicin da ya fi muni tun bayan da aka bayyana cewa an fatattaki 'yan kungiyar IS daga kasar a 2017.

Ana ganin wannan zanga-zanga a matsayin wani babban kalubale ga gwamnatin Firai Minista Adel Abdel Mahdi, kusan shekara daya kenan da fara mulkinsa.

Jami'an kasar dai na ta kokarin takaita zanga-zangar ta hanyar saka dokar hana fita da kuma toshe hanyoyin intanet.