Wadanda ake zargi da taimkon 'yan cirani sun kubuta

Tunusia
Bayanan hoto, Kungiyar masunta a Tunusia ta gudanar da znga-zngr kiran sako abokan aikinsu
An wallafa

An wanke masuntan nan 6 'yan kasar Tunusia da hukumomin kasar Italiya suka cafke, bi sa zargin su na tallafawa 'yan cirani da ke shiga turai ba bisa ka'ida ba.

Lauyan daya daga cikinsu, da kungiyar masuntan Tunusia ne suka tabbatarwa BBC.

A watan da ya gabata dai an gudanar da zazzafar zanga-zanga, wadda kungiyar masunta ta jagoranta sakamakon kama abokan sana'arsu.

Magoya bayan wadanda ake zargin a garin Zarzis da ke gabar teku a kudu masu yammacin kasar sun ce mutnen sun taimkawa wadanda ke tsananin bukatar taimako ne sakamakon kwale-kwalen da suke ciki na neman tuntsurawa.

A lokacin dai wani kwale-kwalen masu fasa kwaurin mutane dauke da 'yn cirani 14 ne y fuskanci tangarda akan hanyarsa ta isa tsuburin Lamfadusa na Italiya.

Daya daga cikin 'yan ciranin da suka kubuta, ya shaidawa BBC cewa su na ta gararanba a cikin teku a lokacin da injin kwale-kwalen da suke ciki ya mutu.

Dan haka ne masunta suke kokarin taimaka musu da lallashin su koma kasar Tunusia amma suka ki dan haka suka janyo su zuwa gabar Italiya ta yadda masu gadin teku za su gan su tare da dauke su to a lokacin ne aka kama har da masuntan.

Sabuwar gwamnatin Italiya dai ta na daukar tsauraran matakai kan 'yan cirani, wanda kasar ce hanyar da ake bi dan isa kasashen turai.

Harwayau, Italiya na son ganin sauran kasashen tarayyar turai su dauki dawainiyar 'yan cirani da ake tsare da su a cibiyoyin da ke iyakokin kasashen.