BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
Mun sa hannu kan takardar sadaukar da ɗaya bisa uku na dukiyar mahaifinmu - Halima Ɗangote
Arzikin attajirin dai ya kai dala biliyan 35.1, wanda ke nufin idan har wannan adadin ya ci gaba da kasancewa haka, kashi ɗaya bisa uku na dukiyarsa zai kai kusan dala biliyan 11.7.
Za mu yi wa Iran luguden wuta - Trump
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 29 ga watan Yulin 2026.
Me ya sa yawancin mutanen da ke tara ƙwanji ke mutuwa da wuri?
Wani bincike ya gano cewa ƙwararrun masu gina jiki da tara ƙwanji sun fi masu yin motsa jiki na nishaɗi jefi-jefi fuskantar haɗarin mutuwa ta farat-ɗaya sakamakon bugun zuciya.
Da gaske ne INEC ba ta nuna son kai a aikinta?
A baya-bayan nan INEC na fuskantar zarge-zargen nuna son kai a ayyukanta, musamman wasu matakai da take ɗauka, waɗanda a wasu lokuta suke janyo ce-ce-ku-ce a ƙasar.
Ƙasashe 10 masu ƙarancin mutuwar aure a duniya
Amma ya kamata a sani cewa ƙarancin mutuwar aure a wata ƙasa ba shi ne ke nufin cewa ma'aurata sun fi zaman lafiya ba.
Shin ƙarancin makamai ne ya sa Amurka ta dakatar da yaƙi da Iran?
Gwamnatin Amurka ta ce zuwa yanzu yaƙin ya laƙume dala biliyan 37.5, inda mafi yawan kuɗin suka tafi wajen saye da amfani da makamai.
Me ya sa ake yawan samun rikici a mahaƙar ma'adinai a Najeriya?
Al'ummar garin Randagi da kewaye a yankin karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna na cikin tashin hankali sakamkon aukuwar wani rikici da ya ɓarke tsakanin wasu bangarori na manyan masu haƙar ma'adinai.
Yadda muka yi ƙoƙarin sasanta Iran da Amurka a gasar Kofin Duniya - Infantino
Shugaban Hukumar kwallon ƙafa ta Duniya Gianni Infantino ya musanta wasu manya-manyan ruɗani da aka samu lokacin wasan tare da yaba wa Iran kan halartar gasar duk da rikicin da ke tsakaninta da ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi Amurka.
Yadda dillalan miyagun ƙwayoyin Mexico suka kafa cibiya a Najeriya
An gurfanar da wasu ƴan Mexico uku da ƴan Najeriya bakwai, hannayensu ɗaure da ankwa, yayin da mai shari'a Musa Kakaki ke duba sinadarai da kayan aiki, an zarge su da yin amfani da su wajen sarrafa miyagun ƙwayoyi da sinadarin methamphetamine, da aka fi sani da meth.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Safe, 05:29, 30 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Yamma, 19:29, 29 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 29 Yuli 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 29 Yuli 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Wane sauyi Infantino ke son kawowa Fifa da Kofin Duniya?
Wannan shafi ne da yake kawo muku labaran wasannin BBC Hausa na ranakun 27 ga watan Yuli, zuwa 2 ga watan Agusta 2026.
Me ya sa kowace ƙasa ke son doke Najeriya?
Duk da ƙara faɗaɗa gasar, amma Najeriya ita ce tawagar da har yanzu kowa yake son ya samu nasara a kanta.
Barcola na son zuwa Liverpool, Bayern ba ta son rabuwa da Diaz
Ɗanwasan PSG's Bradley Barcola ya amince ta fatar baki ya koma Liverpool, Real Madrid ba ta da niyyar sayar da Vinicius Jr, yayin da Everton ke son kusan fam miliyan 70 kan Iliman Ndiaye.
An naɗa Zidane a matsayin kocin Faransa
Didier Deschamps, kocin tawagar Faransa mafi daɗewa ya kammala aikin da ya kwashe shekara 14 yana yi a tawagar bayan cire Faransa da Spain ta yi a wasan kusa da na ƙarshe na Gasar Kofin Duniya ta 2026.
Me ya sa ake nuna wa tawagar ƙwallon ƙafar Argentina tsana?
"Baya ga kwallon ƙafa siyasar duniya ta shafi farin jinin Argentina".
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Me ya sa Amurka ke goyon bayan ƙasashen da ke ficewa daga Kotun ICC?
Kotun ICC ta daɗe tana fuskantar ƙalubalen ficewar wasu daga cikin mambobinta kuma yanzu tana cikin wani rikici na neman sabon babban mai gabatar da kara, bayan korar Karim Khan.
Masu riƙe da muƙamai 5 da aka taɓa yin garkuwa da su a arewacin Najeriya
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce tana ci gaba da ƙoƙarin ceto Alƙalin Babbar Kotu a jihar Kebbi Mai shari'a Faruku Hassan Bunza da ƴanbindiga suka sace.
Manyan birane 10 da suka fi daɗin zama a duniya a 2026
Mujallar The Economists kan yi nazarain abubuwa a biranen da suka haɗa da kwanciyar hankali da tsarin kiwon lafiya da al'adu da muhallai da ilimi da kuma abubuwan more rayuwa kafin tantance matsaytin da zai bai wa kowane birni.
Trump da Netanyahu sun gana a Fadar White House
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 28 ga watan Yulin 2026.
Ciwon hanta da hanyoyin kamuwa da shi
Likitoci na shawartar al'umma da su rinƙa zuwa gwajin cutar domin ba kasafai take nuna alamu ba kafin ta yi tsanani.
Yadda budurwa ta yanke mazakutar saurayinta a Kano
Abin mamaki ba ya ƙarewa, inda wata matashiya mai shekaru 25 ta yanke mazakutar saurayinta mai shekaru 25 gabaɗaya a yayin da yake bacci a dakin otal da suka kama a Kano.
Zanga-zangar matasa da ta tilasta wa ministan ilimi murabus a Indiya
Abin da ya sa murabus ɗin ministan ilimi Dharmendra Pradhan bayan shafe fiye da mako guda ana zanga-zanga mai zafi a titunan ƙasar, ya zama wani muhimmin al'amari a siyasar India.
Zarge-zarge 5 da shugaban Nijar ya yi kan Faransa da ƙasashe maƙwafta
Cikin wata hira da manema labarai a wani ɓangaren na cikarsa shekara uku kan karagar mulki, Janar Tchaini ya ce Faransa ce ke kitsa mafi yawan ayyukan ta'addanci a ƙasar.
Yadda ƴanbindiga suka bi gida-gida suna 'kashe mutane' a Kauru
Bayanai sun ce ƴan bindiga ne waɗanda yawansu ya kai kimanin da 50 suka afka wa ƙauyen Chawai da ke ƙaramar hukumar Kajuru, suka kashe mutane tare da raunata wasu da dama.
Yadda ambaliyar ruwa ta fara ɓarna a arewacin Najeriya
Ambaliyar ta ruguza gidajen jama'a da dama a garuruwan Janbango da Dangamau da kuma Kusada a jihar Katsina, lamarin da ya bar iyalai da dama ba tare da matsuguni ba, baya ga rashin abinci da sutura.
Wane ne asalin wanda ya kafa jam'iyyar ADC?
Su wane ne suka kafa jam'iyyar, kuma wace rawa ta taka a zaɓukan baya, sannan su wane ne suka riƙe ta zuwa yanzu?
A halin yanzu ba ma tattaunawa da Amurka - Iran
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2026.
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































