KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 27 ga watan Yunin 2026.

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Najeriya ta yi martani kan kisan ɗan ƙasarta a Afrika ta Kudu

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya, ta hannun ofishin jakadancinta da ke Johannesburg, ta yi allawadai da kisan wani ɗan ƙasarta, Ibeh Chika Simon, wanda ya mutu a yayin wani samamen da 'yansandan Afirka ta Kudu suka kai a Bellville da ke Cape Town a ranar 23 ga Yuli.

    Jakadancin ya ce mutuwar tasa ta faru ne a yanayi mai cike da tambayoyi, yayin da kuma wani ɗan Najeriya, Egwabor Patrick Chuks, ya samu munanan raunuka bayan an harbe shi a wannan samame.

    A wata sanarwa, ofishin jakadancin ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da yadda lamarin ya faru, yana mai zargin jami’an tsaro da amfani da matakan da suka kai ga mutuwar marigayin.

    Haka kuma, ya bayyana lamarin a matsayin wani ɓangare na abin da ya kira ci gaba da kashe-kashen da ba a warware ba da kuma zargin cin zarafin baƙi a Afirka ta Kudu.

    Najeriya ta buƙaci hukumomin ƙasar su gudanar da bincike cikin gaggawa, adalci da gaskiya tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

    A nata ɓangaren, Kwamitin Ministoci kan Harkokin Hijira na Afirka ta Kudu ya ce ana ci gaba da binciken abin da ya faru.

    Ministar Shari’a Afrika ta Kudu, Mmamoloko Kubayi, ta ce a yayin samamen ƴansandan, wasu mutane sun yi turjiya ga jami’an tsaron yayin da kuma wasu baƙi suka hana su gudanar da aikinsu.

    Ta ce za a bayyana sakamakon binciken idan an kammala shi, tare da ƙara da cewa gwamnati na damuwa da hare-haren sintiri da ake kai wa baƙi, inda aka kama mutum bakwai da ake zargi da hannu a irin waɗannan ayyuka

  2. Kare Lebanon shi ne sharaɗin farko a yarjejeniyar Iran da Amurka - Mojtaba

    ....

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Kafofin yaɗa labarai na Iran sun wallafa wata wasiƙa da suka ce Mojtaba Khamenei ne ya aike ta a matsayin martani ga wasiƙar shugaban Hezbollah na Lebanon da kuma mubaya’arsa gare shi.

    A cikin wasiƙar, Mojtaba Khamenei ya yabawa Hezbollah, yana mai bayyana ƙungiyar a matsayin jagorar ƙungiyoyin jihadi masu yaƙi da Isra'ila.

    Wasiƙar ta ce Iran ta ɗauki kare Hezbollah a Lebanon a matsayin wata muhimmiyar manufa ta dabarun siyasa, bisa tsarin da Ali Khamenei ya shimfiɗa.

    Haka kuma, ta bayyana cewa kiyaye cikakken ikon ƙasar Lebanon da kuma janyewar Isra'ila gaba ɗaya daga yankunanta ba tare da wani sharadi ba su ne manyan sharuɗɗan yarjejeniyar da ake son amfani da ita wajen kawo ƙarshen yaƙin Iran da Amurka.

    Rahotanni sun ce tun bayan harin da Amurka ta kai kan gidan Ayatollah Ali Khamenei da iyalansa a ranar 29 ga Maris, ba a sake ganin Mojtaba Khamenei ko jin muryarsa ba.

  3. Amurka na aika mana saƙonni amma fifikonmu shi ne kare ƙasarmu - Iran

    Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, ya ce Amurka na ci gaba da aika wa Iran saƙonni, amma abin da ƙasarsa ta fi mayar da hankali a kai shi ne kare yankinta, ikon mallakarta da kuma al'ummarta.

    Baghaei ya zargi Amurka da Isra'ila da kai hare-hare kan Iran sau biyu a baya yayin da ake tattaunawa tsakanin ɓangarorin, yana mai cewa hakan ya nuna an ci amanar diflomasiyya sau uku.

    Ya kuma ce Amurka ta karya yarjejeniyar fahimtar juna da aka cimma, yayin da Shugaban Amurka Donald Trump ke zargin Iran da rashin cika alkawurran da take ɗauka.

    Bayan kusan kwanaki biyu da dakatar da hare-haren ramuwar gayya tsakanin Iran da Amurka, rahotanni na nuna yiwuwar sake komawa teburin tattaunawa domin kawo ƙarshen rikicin.

  4. Assalamu alaikum!

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Litinin daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ke fatan saka kasancewa da ku a wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.