Robert Lewandowski ya lashe takalmin zinare a nahiyar Turai karo biyu a jere

Robert Lewandowski

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Robert Lewandowski shi ne kan gaba a cin kwallaye a nahiyar Turai a kakar 2021/22, hakan ya sa ya lashe kyautar takalmin zinare a bana.

Dan kwallon Bayern Munich ya ci 35 a raga a Bundesliga, hakan ya sa ya samu maki 70, shi ne wanda ya karbi kyautar a bara.

Dan wasan Paris Saint-Germain, Kylian Mbappé ne na biyu mai kwallo 28 da ya hada maki 56, yayin da Ciro Immobile na Lazio da Karim Benzema na Real Madrid kowanne ya ci kwallo 27, kenan kowanne ya hada maki 54.

Lewandowski ya lashe kyautar takalmin zinare karo na biyu a jere, bayan da ya zura kwallo 41 a Bundesliga a kakar 2020/21.

An fara bayar da kyautar wanda ke kan gaba a cin kwallaye a Turai tun daga 1968, an kuma ci karo da tsaiko a 1990 daga nan aka ciga kamar yadda aka saba.

Kyautar ana bayar da ita ga duk wanda ya ci kwallo fiye da kowa a gasar mambobin hukumar kwallon kafar Turai, UEFA a kakar tamaula.

Wani dan wasan Bayern Munich da ya lashe kyautar karo biyu shi ne Gerd Muller a kakar 1969/70 da kuma 1971/72.