Paul Pogba zai bar Manchester United a karshen kakar bana

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Paul Pogba zai bar Manchester United a karshen watan Yuni da kwantiraginsa zai kare a Old Trafford, kamar yadda kungiyar ta sanar.

United ta sayi dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 29, wanda ya lashe kofin duniya kan fam miliyan 89 daga Juventus a 2016 a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Pogba ya fara zuwa Old Trafford daga Le Havre ta Faransa a 2009 a matakin dan shekara 16 da haihuwa, yana cikin matasan kungiyar da suka dauki Youth Cup a 2011.

Ya buga wa babbar kungiyar wasa bakwai daga nan kwantiraginsa ya kare a Yulin 2012, sai ya koma Juventus da taka leda.

Pogba ya lashe kofi takwas a Juventus har da Serie A hudu, daga nan United ta sake daukar shi a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya.

Ya dauki League Cup da Europa League a kakar farko a Old Trafford, amma bai samu damar daukar wasu kofunan ba a kaka ta biyu ba.

Pogba ya ci kwallo 39 a wasa 233 a kaka biyun da ya yi, sai dai kuma a wasan karshe a Premier League da Norwich City a Old Trafford, magoya bayan United sun yi ta masa kuwa da ta kai aka sauya shi a ranar.