'Yan wasan Premier League da kwantiraginsu zai kare a bana

Asalin hoton, Reuters
Ranar 30 ga watan Yuni karshen yarjejeniyar 'yan wasan Premier League za ta cika, hakan zai bai wa wasu 'yan kwallon damar gwada sa'a a wata kungiyar a badi kenan.
Cikin jerin fitattun kungiyoyin Premier League, Manchester United tana da 'yan wasan da za su bar kungiyar a karshen kakar nan.
'Yan kwallon sun hada da Paul Pogba da Jesse Lingard da Edinson Cavani da kuma Juan Mata, kenan za a iya daukarsu a matakin wadanda ba su da yarjejeniya kenan.
Duk kungiyar da ke son rike dan kwallonta kan sake kulla yarjejeniya, kafin shekara daya da wa'adin da suka kulla ya cika, idan ba a samu hakan ba - dan wasan ya zama mara kungiya kenan a kakar gaba.
Kuma tun kan shekara dayan ta cika, idan ba su cimma yarjejeniya ba, zai iya tattaunawa da wasu kungiyar kan batun komawa can da taka leda.
Wasu kuma 'yan kwallon kan amince da tayin wasu kungiyar inda da zarar kakar ta kare sai su koma kungiyar da suke so a matakin mara kungiya, mara yarjejeniya - kuma hakan hasara ce ga gungiyar da ya bari - wadda ya koma ta dauki arha.
Sai dai kungiya ko dan wasa kan sauya shawara su kulla yarjejeniya a tsakaninsu, amma yawanci idan aka kai wannan matakin, kodai dan wasan ya gaji da kungiyar ko ita ke son rabuwa da dan kwallon.
Shi dai Pogba, mai shekara 29 an yi ta alakanta shi da Paris St German ko Barcelona ko Real Madrid ko kuma tsohuwar kungiyarsa Juventus.
United ta kare a mataki na shida a Premier League, ta kuma dauki Erik ten Haag, domin daga darajar kungiyar, wadda ke yin baya a kwazon da aka santa a baya.
Jerin 'yan wasan Premier League da kwantiransu zai kare a bana:
Paul Pogba (Man Utd)
Antonio Rudiger (Chelsea)
Andreas Christensen (Chelsea)
James Tarkowski (Burnley)
Alexandre Lacazette (Arsenal)
Jesse Lingard (Man Utd)
Christian Eriksen (Brentford)
Divock Origi (Liverpool)
Eddie Nketiah (Arsenal)
Roman Saiss (Wolves)
Jeffrey Schlupp (Crystal Palace)
Daniel Amartey (Leicester)
Pascal Gross (Brighton)
Jordan Ayew (Crystal Palace)
Jonjoe Kenny (Everton)
Edinson Cavani (Man Utd)
Nemanja Matic (Man Utd)
Nicolas N'Koulou (Watford)
Ben Mee (Burnley)
Andriy Yarmolenko (West Ham)
Juan Mata (Man Utd)
Joao Moutinho(Wolves)
Loris Karius (Liverpool)
Danny Welbeck (Brighton)
Fabian Delph (Everton)
Angelo Ogbonna (West Ham)
Fernandinho (Man City)
James Milner (Liverpool)
Ashley Young (Aston Villa)











