An taba yi min barazanar harin bam - Harry Maguire

An wallafa

Harry Maguire ya ce ya kan karbi duk wata suka da ake yi masa kan rashin sa kwazo a lokacin da yake taka leda.

To sai dai kuma an wuce makadi da rawa a lokacin da ya karbi sakon harin bam tun a farkon shekarar nan.

Cikin watan Afirilu 'yan Sanda sun share gidan dan kwallon Manchester United da tawagar Ingila, inda yake zauna da budurwarsa da yara biyu, sakamakon barazanar da aka yi masa.

Mai shekara 29 ya ce ''Na yi girman da nake karbar shawara, idan an bukaci na kara kwazo a wasannin tamaula.

''Akwai abin da za a yi maka ya wuce misali, domin ni mutum ne ina kuma da iyali.''

Maguire ya kara da cewar: ''Mutane kan tambaye ni ko hakan kan shafi rayuwa ta. Ni dai abin baya damuna sosai, amma da aka yi maganar harin bam, abu ne da ya shafi iyalai na.

''Ina cike da farinciki, yara na kana na ne, ba za su iya karatu ba ko karanra wasu labarai.

''Da yara na manya ne, za su san me yake faruwa, domin za su je makaranta, kuma mutane za su yi ta magana kan batun da zai je kunnensu. Anan ne abin zai dan dame ni.''

Maguire ya kara da cewar ''Na fuskanci kalubale a kakar 2021/22, inda United ta yi ta shida a teburin Premier, kaka mafi munu da ta samu maki mafi karanci a tarihin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Tsohon mai tsaron bayan Leicester City ya sha suka da caccaka kan yadda yake taka leda, amma ya yadda hakan ya biyo bayan da yake kwararren dan kwallo ne.

''Gaskiya na fuskanci kalubale a kakar da aka kammala - ba wani batu bane da za a boye in ji Maguire.

''An fi yin korafi a kaina, koda yake da wadanda suka fuskanci kalubalen tamaula da yawa, amma nine aka fi caccaka.

''Sai dai kowacce rana ina ta kokarin gyara kurakure na, wannan kakar na fuskanci kalubale mai yawa a fannin sana'ar taka leda.

''Duk wanda ke buga tamaula shekara 10 zuwa 15, idan har kana son kai wa kololuwa, dole ka fuskanci dadi da kuma bacin rai a rayuwa.''

Magoya bayan tawagar Ingila sun yi wa Maguire ihu a wasan sada zumunta da tawagar ta casa Ivory Coast 3-0 a cikin watan Maris.