Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Harry Maguire: Dan wasan zai iya fuskantar Norwich
An wallafa
Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce dan wasansa na baya Harry Maguire zai iya dawo wa murza leda a wasansu da Norwich a ranar Asabar.
Maguire mai shekaru 26, ya ji rauni a kafarsa lamarin da ya hana shi buga wasansu na tsakiyar mako tare da Manchester City a gasar cin kofin Carabao.
"Harry zai iya buga wasanmu na gobe," in ji Solskjaer.
"Raunin ba mai tsanani bane."
Sai dai Solskjaer ya ki cewa komai kan batun watakila Ashley Young ya koma Inter Milan a wannan watan.