Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kevin de Bruyne ne gwarzon dan wasan Premier League na 2021/22
Dan wasan Manchester City, Kevin de Bruyne ya lashe kyautar gwarzon dan wasan gasar Premier League na 2021/22.
Haka kuma takwaransa, Phil Foden ne matashin dan kwallon da ba kamarsa a babbar gasar tamaula ta Ingila ta kakar nan.
De Bruyne ya ci kwallo 15 ya bayar da bakwai aka zura a raga a bana, wanda City ke mataki na daya kafin buga karawar karshe ranar Lahadi.
Foden, mai shekara 21, ya zama na farko da ya lashe kyautar karo biyu a jere a tarihi.
An zabi De Bruyne, mai shekara 30 gwarzon bana, bayan zaben da aka gudanar a shafin intanet na Premier League da kyaftin-kyaftin din kungiyoyi 20 da kuma wasu masana harkokin tamaula.
Sauran da suka yi takara sun hada da Joao Cancelo na Manchester City da 'yan wasan Liverpool, Mohamed Salah da Trent Alexander-Arnold da Jarod Bowen na West Ham.
Dan kwallon Arsenal, Bukayo Saka da Son Hueng-min na Tottenham da na Southampton, James Ward-Prowse duk suna cikin 'yan takarar.
De Bruyne ya fara lashe kyautar a 2019-20, hakan ne ya sa ya bi sahun Thierry Henry da Cristiano Ronaldo da Nemanja Vidic wadanda suka karba karo biyu.
Foden, wanda ya ci kwallo tara da bayar da biyar aka zura a raga ya lashe kyautar karo na biyu kuma a jere a matakin fitatcen matashi dan kasa da shekara 23 da ba kamarsa a Premier League ta bana.
Dan wasan tawagar Ingila ya yi takara tare da Alexander-Arnold na Crystal Palace mai buga wasannin aro daga Chelsea da Conor Gallagher da na Palace, Tyrick Mitchell.
Sauran sun hada da Mason Mount na Chelsea da na Arsenal, Aaron Ramsdale da Saka da kuma dan kwallon West Ham, Declan Rice.