Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo da Haaland

An wallafa

Har yanzu ba a samu wani ci gaba ba game da bukatar Saul Niguez ta barin Atletico Madrid domin ya tafi Barcelona kuma wakilin dan wasan tsakiyar na Sifaniya yana ta tuntubar kungiyoyi, inda ake hasashen dan wasan, mai shekara 26, zai koma Liverpool ko Manchester United.

Cristiano Ronaldo ya wallafa "ranar daukar mataki" a shafinsa na Instagram kwana guda bayan jaridar L'Equipe ta bayar da rahoton cewa tafiyar dan wasan Argentina Mauro Icardi, mai shekara 28, daga Paris St-Germain zuwa Juventus ta dogara ne kan ko dan wasan Portugal, mai shekara 36, zai bar Juve ko kuma a'a.

Arsenal ta shirya bai wa Sassuolo £34m kan dan wasan tsakiyar Italiya Manuel Locatelli, mai shekara 23.

Chelsea ba "za ta yi kasa-a-gwiwa" a kokarinta na daukar dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland, mai shekara 20, ko da yake damar yin musayar dan wasan na Norway kalilan ce.

Kazalika Chelsea ta nemi yin musayar dan wasan Ingila Callum Hudson-Odoi, mai shekara 20, da dan wasan Bayern Munich dan kasar Faransa mai shekara 25 Kingsley Coman. (L'Equipe - in French)

Arsenal ta shiga fafatawar neman dan wasan Norwich dan shekara 21 Max Aarons - wanda ake hasashen zai tafi Bayern Munich - inda aka ce Gunners na son samun dan wasan da zai maye gurbin dan kasar Sifaniya Hector Bellerin, 26.

Everton na dab da daukar dan wasan Ingila Andros Townsend, mai shekara 30, wanda ba shi da kungiya tun bayan barin Crystal Palace kuma zai zama dan wasa na farko da Rafael Benitez zai dauka a matsayinsa na kocin Toffees. Kazalika kungiyar tana son daukar dan wasan Bayer Leverkusen dan kasar Ingila Demarai Gray, mai shekara 25.

Everton ta bi sahun kishiyarta ta Gasar Firimiya, West Ham, wajen mika bukatar daukar dan wasan Barcelona mai shekara 26, Clement Lenglet.

Dole ne Juventus ta biya £43m idan tana son daukar dan wasan Brazil Gabriel Jesus daga Manchester City. Kungiyar ta Serie A tana matukar son daukar dan wasan mai shekara 24, wanda saura shekara biyu kwangilarsa ta kare a City

Juventus na son karbo aron dan wasan Paris St-Germain dan kasar Argentina Leandro Paredes, mai shekara 27, domin ya cike gurbin dan wasan Brazil Arthur Melo, mai shekara 24, wanda yake fama da rauni.

Barcelona na sha'awar daukar aron dan wasan Lille da Portugal Renato Sanches da kuma zabin sayensa. An sanya farashin £30m kan dan wasan mai shekara 23, wanda da wahala Barca ta iya biya.