Tottenham 3-0 Arsenal: Saura maki daya tsakanin Arsenal da Tottenham

An wallafa

Tottenham ta rage tazarar maki da ke tsakaninta da Arsenal ya koma saura daya, bayan da ta doke Gunners 3-0 a kwantan wasan Premier da suka fafata ranar Alhamis.

Minti 22 da fara wasa Harry Kane ya ci wa Tottenham kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan ya kara na biyu daf da za su je hutu.

Heung-min Son ne ya kara na ukun da ya bai wa Tottenham hada maki ukun da take bukata a wasan na hamayya na kungiyoyin cikin Landan.

Kawo yanzu Son ya ci kwallo 21 a kakar Premier ba tare da bugun fenariti ba, Kane ne a Tottenham ya kafa tarihi a babbar gasar tamaula ta Ingila da cin kwallo 28 a 2017-18 da zura 24 a raga a 2016-17 duk ba tare da cin fenariti ba.

Karon farko kenan da Tottenham ta zura kwallo har uku a ragar Arsenal ba tare da ta zare ko daya ba a tarihin haduwarsu tun bayan 5-0 a Afirilun 1983.

Haka kuma karon farko da Tottenham ta doke Arsenal a wasa uku a jere, rabon da ta yi wannan bajintar tun Agustan 1961.

Arsenal din ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Rob Holding jan kati, ya zama na 13 da aka kora a wasa daga Gunners tun bayan wanda aka bai wa Mikel Arteta jan kati a wasansa na farko a kungiyar.

Da wannan sakamakon Arsenal tana mataki na hudu a kan teburi da maki 66, ita kuwa Tottenham tana ta biyar da tazarar maki daya tsakaninta da Gunners.