Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Salah, Solskjaer, Taylor, Chalobah
Dan kwallon tawagar Masar mai taka leda a Liverpool, Mohamed Salah, na son a rinka biyansa fam 500,000 a kowanne mako idan ana son ya ci gaba da taka leda a Anfield. (Football Insider)
Ole Gunnar Solskjaer, na kokarin yadda zai tsira da aikinsa na kocin Manchester United, bayan da mahukuntan kungiyar suka fara gajiya da rashin kokarinsa tun kan wasan da Liverpool ta doke United a Old Trafford ranar Lahadi a gasar Premier League. (ESPN)
Masu kungiyar Manchester United na duba yadda za su kori Solskjaer, kafin wasan Premier da za ta fafata da Tottenham ranar Asabar. (Manchester Evening News)
Zinedine Zidane, bai da sha'awar karbar aikin horar da tamaula a Old Trafford, duk da cewar baya komai tun bayan da ya bar kocin Real Madrid cikin watan Mayu. Mai shekara 49 na fatan horar da ko dai Paris St-Germain ko kuma tawagar Faransa gurbin da wasu ke aiki kawo yanzu. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Newcastle United ta mai da hankali kan yadda za ta dauki dan kwallon Aston Villa, Marvelous Nakamba, a cikin watan Janairu. (Football Insider)
Barcelona, Ronald Koeman, zai tsinci kansa cikin matsi da fuskantar kalubale idan aka ci kungiyar wasa uku a jere nan gaba. (Marca)
Dan kwallon tawagar Netherlands, Donny van de Beek, ya yanke shawarar canja wakilinsa,bayan da yake son barin Manchester United wanda Everton da Newcastle da kuma Juventus ke son dauka.. (Metro)
Tottenham da Aston Villa da kuma Everton na son daukar dan wasan Stoke City, Harry Souttar. (Football Insider)