Marcelo ya cika shekara 34 da haihuwa

Asalin hoton, Real Madrid FC
Mai tsaron bayan Real Madrid, Marcelo na bikin cika shekara 34 da haihuwa.
Tuni dan wasan tawagar Brazil ya zama gwarzo a Real Madrid, bayan rawar da yake takawa da gudunmuwar da yake bayarwa a kungiyar da ke da Champions League 13.
An haifi Marcelo ranar 12 ga watan Mayun 1988 a Rio de Janeiro, ya kuma fara yi wa Real wasan farko ranar 7 ga watan Janairun 2007 a karawa da Deportivo a filin wasa na Riazor.
Yana cikin 'yan wasan da suka lashe La Liga na bana kuma kofi na 24 da ya dauka a Real Madrid, shi ne kan gaba a yawan daga kofi a kungiyar.
Dan kasar Brazil ya yi wa Real Madrid wasa 545 a kaka 16 da ya yi a kungiyar da cin kwallo 38.
Kyaftin din Real Madrid ya lashe Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu da European Super Cups uku da La Liga shida da Copas del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups biyar.
Real ce ta ci La Liga na bana kuma na 35 jumulla, za ta buga wasan mako na 36 da Levante a gasar La Liga ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.
Real Madrid da Liverpool za su buga wasan karshe a Champions League na bana ranar 28 ga watan Mayu a Faransa, watakila Marcelo ya dauki kofi na 25 a kungiyar ta Sifaniya.









