Real Madrid 6-0 Levante: Real Madrid ta ci Levante 6-0.

An wallafa

Real Madrid ta casa Leavante da ci 6-0 a wasan mako na 36 a gasar La Liga da suka fafata ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.

Ferland Mendy ne ya fara cin kwallo a minti na 13 da take leda, minti shida tsakani Karim Benzema ya kara na biyu, sannan Rodrygo ya zura na uku a raga.

Daga baya ne Vinicius Junior ya ci uku rigis a karawar.

Da wannan sakamakon, Real Madrid wadda ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana, kuma na 35 jumulla, tana ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona mai biye da ita.

Ita kuwa Levante mai maki 29 tana ta biyun karshe wato ta 19 a kasan teburin kakar bana.

'Yan wasan da koci, Carlo Ancelottiya ya fuskanci Levante da su a Santiago Bernabeu a wasan na mako na 36.

'Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Fuidias.

Masu tsaron baya: E. Militão, Vallejo, Nacho, F. Mendy da kuma Gila.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, L. Vázquez, Camavinga da kuma Peter.

Masu cin kwallaye: Benzema, Jović, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.