Real Madrid za ta fafata da Levante a La Liga ranar Alhamis

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid da Levante za su fafata a gasar La Liga karawar mako na 36 ranar Alhamis a Santiago Bernabeu.
Tuni dai Real Madrid ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana, kuma na 35 jumulla.
Kungiyoyin sun fara fuskantar juna a gasar bana ranar 22 ga watan Agusta, inda suka tashi 3-3 a gidan Levante.
Wadanda suka ci wa Levante kwallayen sun hada da Roger da Jose Gomez Campana da kuma Rober, yayin da aka yi wa Aitor Fernandez jan kati.
Ita kuwa Real ta ci kwallaye ta hannun Gareth Bale, sannan Vinicius Junior ya zura biyu a raga.
Real Madrid wadda za ta buga wasan karshe a Champions League da Liverpool ranar 28 ga watan Mayu, tana ta daya a teburin La Liga da maki 81.
Ita kuwa Levante mai maki 29 tana ta biyun karshe wato ta 19 a kasan teburin kakar bana.
Tuni Real ta ci gaba da atisaye don fuskantar karawar mako na 36, bayan da 'yan wasa suka motsa jiki, sannan suka murza leda.
'Yan wasa da suka hada da Alaba da Bale da kuma Marcelo sun motsa jiki a waje da cikin fili.
Shi kuwa Ceballos da Carvajal da Asensio sun motsa jiki a rufaffen dakin samun kuzari.








