Barcelona na son daukar Bernardo Silva

An wallafa

An kusan karkare wasannin gasar kasashen Turai ta bana, daga nan za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo don tunkarar badi..

Tun kafin lokacin ana ta jita - jitar motsawar wasu 'yan kwallon tamaula da masu horar da 'yan wasa.

Ga kadan daga cikin labaran da wasu suka wallafa:

Barcelona na son sayen dan lwallon Manchester City, Bernardo Silva, mai shekara 27 dan kwallon tawagar Portugal (Mundo Deportivo)

Liverpool na kan gaban Real Madrid da kuma Chelsea a rige-rigen sayen dan kwallon Monaco mai shekara 22, Aurelien Tchouameni. (Marca via Metro)

Watakila Arsenal ta hakura da zawarcin dan wasa mai shekara 24 na Argentina, Lautaro Martinez, bayan da Inter Milan ba ta da shirin sayar da dan kwallon.(Gazetta Dello Sport)

Kungiyar Arsenal da Chelsea da Manchester United na son daukar dan wasan RB Leipzig, dan kasar Faransa, Christopher Nkunku, mai shekara 24 bayan karshen kakar nan. (Football.London)