Arsenal ta yi kane-kane a mataki na hudu a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na ci gaba da sa kwazo, domin samun gurbin shiga gasar Champions League a kakar badi.
Gunners din ta yi nasarar doke Leeds United da ci 2-1 a wasan mako na 36 da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.
Eddie Nketiah ne ya fara ci wa Gunners kwallo minti biyar da fara wasa, sannan minti biyar tsakani ya kara na biyu.
Leeds United ta farke daya ta hannun Diego Llorente, amma ta karasa karawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Luke Ayling jan kati tun a minti na 27 da fara tamaula.
Da wannan sakamakon Arsenal ta ci gaba da zama a mataki na hudu a teburin Premier League da maki 66 da tazarar maki hudu tsakaninta da Tottenham.
Tottenham abokiyar hamayyar Arsenal ta tashi 1-1 da Liverpool a Anfield ranar Asabar.
Bayan da Leeds ta yi rashin nasara a gidan Gunners da Everton ta je ta ci Leicester City, kenan kungiyar da Jesse Marsch ke jan ragama ta yi kasa zuwa cikin 'yan ukun karshen teburi.








