Champions League: Liverpool ta kai wasan ƙarshe bayan guje wa abin kunya a Villarreal

Liverpool da Villareal

Asalin hoton, Uefa

Bayanan hoto, Liverpool ta farke ƙwallo biyun da aka ɗura mata a farkon wasan tare da cinye shi 2-5 gida da waje
An wallafa

Liverpool ta farke ƙwallon biyun da Villarreal ta ɗura mata a gasar Zakarun Turai ta Champions League tare da ci gaba da fatan lashe kofi huɗu a kakar bana.

Ƙungiyar ta yi nasara a wasan farko na karawar da aka yi a Ingila da ci 2-0 amma kuma ta shiga ruɗani bayan minti 41 da take wasa na biyun a Spaniya a daren Talata.

Boulaye Dia ne ya ci wa Villarreal ƙwallon farko a minti na uku da take wasa, kafin daga baya tsohon ɗan wasan Arsenal Francis Coquelin ya ƙara ta biyu.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma Fabinho ya farke wa Liverpool ɗaya, sai kuma Luis Diaz wanda aka sako daga baya ya farke musu da ƙwallon da ya ci da ka.

Sadio Mane ne ya rufe wasan ƙwallonsa wanda ya bai wa Liverpool ɗin damar zuwa wasan ƙarshe a Champions League sau uku cikin shekara biyar - ta cinye wasan da ci 2-5 kenan gida da waje.

Villarreal ta ƙare wasan da mutum 10 a cikin fili bayan an bai wa Capoue jan kati sakamakon kati na biyu da aka ba shi.

Liverpool za ta kara da wanda ya yi nasara a wasan ranar Laraba tsakanin Real Madrid da Manchester City.

Za a buga wasan ƙarshen ranar Asabar, 28 ga watan Mayu a birnin Paris na Faransa.

Babu wata ƙungiya daga Ingila da ta taɓa lashe kofin Champions League, da Premier League, da FA Cup, da kuma League Cup a kaka ɗaya wanda Liverpool ke yunƙurin yi yanzu haka.