Liverpool: 'Babu tabbas' ko Salah da Mane za su ci gaba da zama bayan Klopp ya tsawaita zamansa

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce tsawaita zamansa da ya yi a Liverpool ba shi da alaƙa ko tabbas da ci gaba da zaman Mohamed Salah da Sadio Mane.
A ranar Alhamis Klopp ya tsawaita kwantaragin zamansa a Liverpool da shekara biyu har zuwa 2026, yayin da kwantaragin Salah da na Mane zai ƙare a ƙashen kakar nan.
Da aka tambaye shi game da tasirin da hakan zai yi kan Salah da Mane, Klopp ya ce: "Wannan ya rage ga yaran ko me hakan ke nufi a wajensu. Amma dai ba wata matsala. Alaƙata da su biyun mai kyau ce."
Klopp ya ce: "A rayuwa, akwai abubuwa da yawa da ya kamata a lura da su fiye da maganar wane ne kociya, amma sanin wane ne kocin da muƙarrabansa abu ne mai muhimmanci.
"Abu ne mai ƙarfafa gwiwa ga yaran, amma dai ba na jin wannan zai zama abin yanke hukunci ba game da hukuncin da su za su yanke. Rayuwarsu ce.
"Muna dai so mu tabbatar cewa duk wanda zai ci gaba da zama a nan ya san abin da zai iya samu."
Salah ya ce zai so ya ci gaba da zama a Liverpool kuma ba da jimawa ba ya sake "ba kodayaushe ake yin komai don kuɗi ba".
Shi ma ɗan wasan gaba Roberto Firmino da na tsakiya Naby Keita, yarjejeniyarsu za ta ƙare a ƙarshen kakar nan.
Liverpool wadda ke bin bayan Manchester City da maki ɗaya a saman teburi, za ta ziyarci Newcastle don buga wasan Premier League ranar Asabar.











