Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ralf Rangnick 'ba ya jin dadin' aiki a Man Utd
Kocin rikon-kwarya na Manchester United Ralf Rangnick ya ce "ba ya jin dadi gaba daya" na zamansa a kungiyar inda ya ce ya sa ran jagorantar United zuwa wasan cancantar shiga gasar Zakarun Turai.
United ta doke Brentford da ci 3-0 a wasan baya bayan nan da Rangnick ya jagoranta a gidan kungiyar.
Yanzu haka kungiyar ta shida a saman teburin gasar Firimiya kuma ba za ta samu gurbin shiga gasar Zakarun Turai mai zuwa ba.
"Ba na jin dadin sakamakon da muke samu, musamman a mako hudu zuwa biyar da suka gabata," in ji Rangnick.
An kori tsohon manajan United Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba, inda tsohon dan wasan kungiyar Michael Carrick ya jagorance ta ta buga wasanni uku, sai dai a watan Disamba an dauki tsohon kocin RB Leipzig Rangnick a matsayin kocin rikon-kwarya zuwa karkashe kakar wasa ta bana.
Sai dai United, wadda sau 20 tana zama gwarzuwar gasar Turai, ba ta yi katabus ba a wannan kakar wasan.
Middlesbrough ta bi su har gida ta doke su a zagaye na hudu na gasar cin Kofin FA, sannan tana bayan Manchester City da maki 25 a gasar Firimiya ta Ingila.